Ali Nuhu da Wasu Sabbin Daraktocin Ma'aikatar Al'adu Sun Gana da Minista, Hannatu Musawa

Ali Nuhu da Wasu Sabbin Daraktocin Ma'aikatar Al'adu Sun Gana da Minista, Hannatu Musawa

  • Ministar al'adu, Hannatu Musawa ta gana da wasu daga cikin sabbin daraktocin ma'aikatarta da aka nada
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabbin daraktoci 11 a ma'aikatar raya al'adu ta kasa, ciki harda fitaccen jarumin ma'aikatar Kannywood
  • Shugaban hukumar fina-finan Najeriya, Ali Nuhu ya saki hotunan ganawar tasu a dandalin soshiyal midiya

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Ministar Raya Al'adu ta kasa, Hannatu Musawa ta gana da wasu daga cikin sabbin daraktocin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada a masana'antarta.

Musawa ta karbi bakuncin fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu, Aisha Augie, Otunba Biodun Ajiboye da sauransu a ofishinta dake babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

"Kada ku mayar da kudi Ubangijinku": Tinubu ya ba shugabannin Kirista babban aiki 1 tak

Ali Nuhu ya gana da Hannatu Musawa
Fitaccen Jarumin Kannywood Ali Nuhu Ya Gana da Ministar Al’adu, Hannatu Musawa Hoto: realalinuhu
Asali: Instagram

Ali Nuhu na daya daga cikin daraktocin da Tinubu ya nada, inda zai shugabanci hukumar fina-finai ta Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana cewa sun gana ne kan yadda za su kai ma'aikatar raya al'adu ta kasa zuwa matakin ci gaba

Jarumin fina-finan Hausan ne ya wallafa hotunan ganawar tasu a shafinsa na Instagram.

Martanin jama'a a kan wannan ganawa ta su Ali Nuhu

ali_dawayya ya yi martani:

"Allah ya Kara daukaka da kuma kariyarsa ameen ameen."

gwamnaofficial ya ce:

"Allahu yatemaki sarki @realalinuhu."

zannajr98 ya yi martani:

"Allah sarki bawan Allah mahakurci mawadaci Allah ya dafama ."

mustyfashion1 ya ce:

"masha Allah Allah yayi jagora."

real_umar_uk ya ce

"Masha Allah babanmu ❤️ Allah yakara jagora dan hasken manzan Allah S A W @realalinuhu."

bmaina_fkdain_ ya ce:

"Allah kara maka lafiya da daukaka MD."

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ganawa kan matsalar tikitin Musulmi da Musulmi, Tinubu ya nada dan Arewa babban mukami

thekhalifamuaz ya ce:

"Boko tayi rana Rarara yana Kida kai kuma kana dikar rawa abinka Sarki Allah jaa zamani❤️."

yusufdanmamah_editor ya ce:

"Laaaailaha illahu Babanmu Yasamu❤️❤️ Allah yakaro Dubun Nasara Maigida @realalinuhu ❤️."

Mai daukar hoton Buhari ya fadi yadda ya samu aikin

A wani labarin kuma, Bayo Omoboriowo shi ne mai daukar Muhammadu Buhari hoto a lokacin yana mulki, ya bada labarin yadda ya samu daukaka.

Bayo Omoboriowo bai san kowa ba, amma sai ga shi yana aiki a fadar shugaban kasa, shi bada labarin nan da Channels tayi hira da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel