Rashin Tsaro: Rundunar Soji Ta Saduda, Ta Nemi Agajin EFCC a Wasu Bangarori, Ta Fadi Dalili

Rashin Tsaro: Rundunar Soji Ta Saduda, Ta Nemi Agajin EFCC a Wasu Bangarori, Ta Fadi Dalili

  • Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya nemi hadin kan hukumar EFCC a yaki da ta’addanci da ake fama da shi a Najeriya
  • Musa ya nemi wannan bukata ce a yau Juma’a 15 ga watan Maris a Abuja yayin da ya karbi bakwancin shugaban EFCC, Ola Olukoyode
  • Ya bukaci hukumar da ta taimaka wurin zakulo masu daukar nauyin ta’addanci kamar yadda ta ke kokarin yaki da barna a fadin kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Yayin da matsalar tsaro ke neman fin karfin jami’an soji, rundunar ta nemi hadin kan hukumar EFCC.

Rundunar ta nemi hadin kan hukumar domin zakulo masu daukar nauyin ‘yan ta’adda tare da daukar mataki kansu.

Kara karanta wannan

Azumin Ramadan: Hisbah ta aika da muhimmin gargadi ga wadanda ba musulmai ba a Kano

Yayin da tsaro ke kara ta'azzara, rundunar soji ta bukaci taimako daga EFCC
Rundunar Soji ta nemi taimakon EFCC a Najeriya Hoto: Ola Olukoyode, Janar Christopher Musa.
Asali: Facebook

Hafsun Sojoji ya taya shugaban EFCC murna

Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa shi ya bayana haka a yau Juma’a 15 ga watan Maris a birnin Tarayya Abuja, Cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce zakulo wadanda suke daukar nauyin ta’addanci na daya daga cikin ayyukan rundunar wanda a yanzu suke ci gaba da yi.

Musa ya kuma taya sabon shugaban hukumar murnar samun mukamin shugabancin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa.

Shawarar da Musa ya ba hukumar EFCC

“Da farko ina taya ka murnar samun shugabancin hukumar EFCC, ina tabbatar maka da cewa rundunarmu ba za ta gajiya ba wurin tabbatar da dorewar dmukradiyya.”
“Hanyoyin da kuke bi wurin amfani da fasaha a yaki da cin hanci da sauran badakalar tattalin arziki abin a yaba ne matuka.”

- Christopher Musa

Kara karanta wannan

Arewa ta barke da murna bayan ware $1.3bn kan aikin layin dogo daga Kano zuwa Maradi

Musa ya kuma bukaci EFCC da su karawa masu rike da mukaman siyasa kwarin gwiwar ci gaba da mulki nagari domin inganta tattalin arzikin kasar, cewar Vanguard.

APC ta ba Tinubu shawara

Kun ji cewa jam’iyyar APC ta shawarci Shugaba Tinubu kan yadda zai kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Kungiyar shugabannin jam’iyyar APC a kasar ta ba Tinubu shawarar sallamar dukkan shugabannin tsaron kasar da ba su tabuka wani abu ba.

Wannan na zuwa ne yayin da matsalar tsaro ke kara ta’azzara a Najeriya wanda ke sanadin rasa rayuka da dukiyoyin al’umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.