Yaron Gida Ya Kashe Uwar Dakinsa da Katako Kwanaki 7 da Fara Zuwansa Aiki a Legas

Yaron Gida Ya Kashe Uwar Dakinsa da Katako Kwanaki 7 da Fara Zuwansa Aiki a Legas

  • An shiga tashin hankali a Legas yayin da wani yaron gida ya kashe uwar dakinsa kwanaki bakwai da daukarsa aiki a gidan
  • Yaron gidan ya kashe matar kuma ya jefar da gawarta a saman bene kamar yadda danta da ya kawo ziyara ya gano
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da karin bayani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Legas – Mazauna unguwar Gbagada da ke jihar Legas sun shiga cikin tashin hankali yayin da wani yaron gida ya kashe uwar dakinsa ta hanyar buga mata katako.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, babu wanda zai iya fadin ainihin lokacin da yaron gidan da ya gudu, mai suna Peter, ya aikata laifin.

Kara karanta wannan

"An ba ni su kyauta": Dan Najeriya ya tsinci iPads 500 a shagon da yake aiki

Yaron aiki ya kashe uwar dakinsa a Legas
Yan sanda sun dauki mataki kan yaron aikin da ya kashe uwar dakinsa a Legas. Hoto: @LagosPoliceNG
Asali: Twitter

Sai dai kuma an gano gawar matar ne a ranar Asabar, 9 ga watan Maris, bayan da danta ya kai mata ziyara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin an dade da kashe matar

An ce marigayiyar ita kadai ce ke zaune a cikin gidan amma akwai shaguna uku a gaban ginin.

Wani mazaunin unguwar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

“Na ga lokacin da yaron matar ya ya kawo ziyara gidan, kai tsaye ya nufi dakin mahaifiyarsa, inda ya tarar da gawarta a kan matakalar bene tana kwance cikin jini.
"Amma ko a lokacin, jikinta ya fara kumbura, wanda ke nuna cewa watakila an kashe matar ne tun kwanakin da suka wuce.”

Yaron gida ya gudu

Jaridar ta ruwaito cewa yaron gidan da ya gudu ya fara zuwa aikin ne mako guda kafin afkuwar lamarin.

A halin da ake ciki, an kama wani dan uwan ​​wakilin da ya kawo yaron da ya gudu amma ba a kai ga gano inda asalin wanda ya kawo yaron ba.

Kara karanta wannan

An hargitse a Majalisa kan zargin Sanata Ningi, an fifita manyan Sanatoci wurin rabon kudi

An ruwaito cewa jami'an da ke aiki a ofishin ‘yan sanda na Ifako sun ziyarci inda lamarin ya faru kuma sun tafi da gawar.

'Yan sandan Legas sun dauki mataki

Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce an kama yaron aikin.

Hundeyin ya kara da cewa an mika wanda ake zargin zuwa ga hukumar binciken manyan laifuka ta jihar (SCIID), Panti.

An kama matar da ta ba diyarta guba

A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Legas ta kama wata mata mai suna Rukayat wadda ake zargin ta ba diyar cikinta guba don ta ci ta mutu sakamakon lalurar farfadiya da yarintar take fama da ita.

Kakakin rundunar na jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce an garzaya da yarinyar asibiti domin ceton ranta yayin da kuma aka kama mahaifiyar domin gudanar da bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel