Rashin Tausayi: ‘Yan Sanda Sun Kama Wata Mata da Ta Ba Diyarta Guba

Rashin Tausayi: ‘Yan Sanda Sun Kama Wata Mata da Ta Ba Diyarta Guba

  • 'Yan sanda sun kama wata mata mai suna Rukayat kan sanyawa diyar da ta haifa a cikinta guba a jihar Legas
  • An rahoto cewa matar ta bai wa diyar tata maganin kwari saboda lalurar da ke damunta na farfadiya
  • Kakakin 'yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da tsare matar yayin da ya ce suna kan bincike

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Lagos - Wata mata da aka bayyana sunanta a matsayin Rukayat tana tsare a hannun 'yan sanda kan zargin bai wa diyarta mai shekara daya maganin kwari a yankin Oworonshoki da ke jihar Legas.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na safiyar Juma'a, 8 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Budurwa ta siya katon gida a turai tana da shekaru 22, ta yi murnar zama mai gidan kanta

'Yan sanda sun kama wata uwa a Legas
Diyar matar na fama da lalurar farfadiya Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Me yasa uwa ta ba diyarta guba?

Wata majiya ta 'yan sanda ta bayyana cewa yarinyar na fama da lalurar farfadiya ne kuma cewa mahaifiyar tata ta bata guba ne saboda ta gaji da lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wata Rukayat ta kawo diyarta mai shekara daya da watanni bakwai asibitin LUTH don magani.
"Daga bisani a wannan ranar, sai ta tona cewa ta ba yarinyarta guba da maganin kashe kwari saboda ba za ta iya ci gaba da ace diyarta na da farfadiya ba. Tana so ta huta daga wannan wahalar."

- Majiya ta 'yan sanda

Rundunar 'yan sandan Legas ta magantu

Da aka tuntube shi, kakakin 'yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa an kama mahaifiyar yarinyar kuma ana ci gaba da gudanar da bincike, rahoton Osun defender.

Kara karanta wannan

"Cikar buri": Budurwa ta siya katafaren gida tana da shekaru 26, ta baje kolin cikin gidan a bidiyo

"Jami'an rundunar sun gaggauta tafiya asibitin, sannan sun hadu da yarinyar tana samun kulawar likitoci, kuma an kama mahaifiyar bayan maganin, sannan bincike na gudana."

- Hundeyin

Matar aure ta kashe 'dan kishiyarta

A wani labarin kuma, mun ji cewa jami’an tsaro sun kama wata matar aure mai shekaru 24 kan zargin kashe jinjirin kishiyarta mai kwanaki hudu a duniya da maganin kashe kwari.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakil ne ya bayyana haka a cikin wata sanrwa da ya fitar kuma aka gabatarwa manema labarai a jihar a ranar Talata, 22 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel