Yaron gida ya yiwa babban soja Bahaushe da budurwar sa kisan gilla

Yaron gida ya yiwa babban soja Bahaushe da budurwar sa kisan gilla

Yaron gidan wani babban matashin soja, Laftanal Abubakar Yusuf, ya hallaka shi da budurwar sa, Lorraine Onye, tare da dora laifin abinda ya aikata a kan bacin raid a damuwa.

Yaron gidan, Raphael Jaja, ya shake budurwar Abubakar har saida ta mutu kafin daga bisani ya yi amfani da wuka ya kashe sojan, sannan ya saka gawar sa cikin wata jaka day a dauka zuwa cikin daji inda yak one gawar sa.

Jaja, dan asalin karamar hukumar Opobo-Nkoro ta jihar Ribas ya ce ya kashe maigidan nasa ne da budurwar sa saboda bai biya shi albashin san a tsawon watanni 15 ba amma ya sayawa budurwar ta sa wayar hannu ta N300,000.

Yaron gida ya yiwa babban soja Bahaushe da budurwar sa kisan gilla
Yaron gida ya yiwa babban soja Bahaushe da budurwar sa kisan gilla

Ya kara da cewa marigayi Abubakar ya yi masa alkawarin zai ke tara masa albashin sa (N15,000 a wata) amma kuma ya saba wannan alkawari day a dauka.

Kafin hukumar ‘yan sanda ta bankado gaskiyar abinda ya faru, rahotanni sun bayyana cewar marigayi Abubakar ne ya kasha budurwar ta sa sannan ya gudu ya buya. Amma daga baya binciken hukumar ‘yan sanda karkashin jagorancin jami’in ta, Abba Kyari, ya warware ainihin abinda ya faru.

DUBA WANNAN: Yadda wani ango ya yiwa amaryar sa kisan gilla wata 4 kacal bayan daura masu aure

Hukumar ‘yan sanda ta gano Jaja ne ya aikata laifin bayan gano wayar marigayi Abubakar a hannun wani abokin sa a Fatakwal kafin daga baya su gano inda yak one gawar marigayin da kuma wanda ya sayarwa da motar sa kirar Hyundai a kan naira miliyani N1.9m.

Jaja ya shaidawa wakilin jaridar Punch cewar, ya kashe maigidansa ne saboda ya yi alkawarin bashi miliyan N2.5m bayan ya taimaka masa ya samu wata kwangila ta miliyan N22.8m amma ya gaza cika alkawarin day a dauka kamar yadda ta faru a kan albashin sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel