'Yan sanda sun kama ɗan aikin gida da ya kashe maigidansa a Nasarawa (Hotuna)

'Yan sanda sun kama ɗan aikin gida da ya kashe maigidansa a Nasarawa (Hotuna)

- Rundunar yan sanda a jihar Nasarawa ta tabbatar da kama wani mutum bisa zargin kashe uban gidansa

- Mutumin Cephas Iliya mai shekaru 27, ya shiga komar yan sanda bayan kashe Martins Omeri

- Tuni Kwamishinan yan sandan jihar Bola Longe ya umarci a maida batun sashen binciken manyan laifuka don fadada bincike

Yan sanda a jihar Nasarawa sun kama wani mutum mai shekara 27 mai suna Cephas Iliya, bisa zargin kashe tsohon mai gidansa kamar yadda LIB ta ruwaito.

Mai magana da yawun rundunar, ASP Ramhan Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 26 ga Nuwamba 2020.

Dan aiki ya kashe maigidansa a Nasarawa
Dan aiki ya kashe maigidansa a Nasarawa. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

Nansel ya ce wanda ake zargin, dan asalin jihar Kaduna ya kashe wani Martins Omeri, ma'aikaci a ofishin babban Akanta Janar a Abuja amma mazaunin rukunin gidajen Navy Estate da ke Karshi, karamar hukumar Karu, jihar Nasarawa.

"Ranar 24 ga Nuwamba 2020 da misalin karfe 11:45, jami'an yan sanda da ke ofishin Karshi sunyi bincike na musamman tare da kama wanda ake zargi a unguwar Arab, birnin tarayya Abuja. An gudanar da bincike na tsanaki a bangaren shi kuma an gano kayan mamacin a matsayin hujja: wayar hannu kirar Infinix, Laptop, kayan sawa, takalma, kilifa, kayan gado, da yan kayyaki," a cewar DSP Nansel.

Dan aiki ya kashe maigidansa a Nasarawa
Dan aiki ya kashe maigidansa a Nasarawa. Hoto @lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kotu ta yanke wa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa hukuncin shekaru 3 a gidan maza

Wanda ake zargin ya amsa cewa ya shiga gidan mutumin a daren da zai kashe shi ranar 17 ga Nuwamba 2020 lokacin yana bacci kuma ya kashe shi ta hanyar amfani da katako. An gano gawar ranar 19 ga Nuwamba.

Kwamishinan yan sandan jihar, CP Bola Longe ya umarci a maida batun sashen binciken manyan laifuka CID, don fadada bincike tare da mika wanda ake zargin kotu don ya girbi abin da ya shuka.

Kwamishinan yan sandan ya kuma shawarci mutane da su dinga tantance mutane kafin daukar su yan aiki.

A wani labarin daban, tsohon shugaban majalisar dattawar Najeriya, Sanata Joseph Wayas, yana wata asibiti a birnin Landan sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Wayas shine shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu daga shekarar 1979 zuwa 1983 a lokacin da marigayi Alhaji Shehu Shagari ke shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel