An Shiga Jimami Yayin da Gwamnan APC a Arewa Ya Tafka Babban Rashi, Bayanai Sun Fito

An Shiga Jimami Yayin da Gwamnan APC a Arewa Ya Tafka Babban Rashi, Bayanai Sun Fito

  • Ana cikin jimami yayin da mahaifin matar gwamnan jihar Neja, Hajiya Fatima Bago ya riga mu gidan gaskiya
  • Marigayin Alhaji Muhammad Egba Enagi ya rasu ne a jiya Asabar 9 ga watan Maris a karamar hukumar Edagi
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa za a yi jana'izar marigayin a yau Lahadi 10 ga watan Maris da misalin karfe 2 na rana

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Neja - Mai sarautar gargajiya a yankin Dikko-Enagi, Alhaji Muhammad Egba Enagi ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 90.

Marigayin da aka fi sani da Sarkin Malami Nupe ya rasu ne a jiya Asabar 9 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sanye da kayan sojoji sun kashe mutum 4 a jihar Imo

Gwmanan APC a Arewa ya Tafka babban rashi na suruki
Marigayin ya rasu ne a jiya Asabar a karamar hukumar Edati. Hoto: Umar Bago.
Asali: Facebook

Wanene marigayin ga matar gwamnan Neja?

Marigayin shi ne mahaifin matar Gwamna Muhammad Umar Bago na jihar Neja, Hajiya Fatima Bago.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, Marigayin shi ne mahaifin matar marigayi tsohon gwamnan jihar, Abdulkadir Kure, cewar Leadership.

Rahotanni sun tabbatar cewa za a gudanar da jana'izarsa a yau Lahadi 10 ga watan Maris da misalin karfe 2 na rana.

Za a gudanar da jana'izar ce a a gidansa da ke Dikko-Enagi da ke karamar hukumar Edati da ke jihar, cewar Housing TV Africa.

Dan bindiga ya mutu yayin daukar kudin fansa

Rundunar ‘yan sanda a jihar Neja ta sanar da kisan wani dan bindiga yayin da yaje daukar kudin fansa a jihar.

Rundunar ta ce ta yi nasarar bindige dan bindigar a karamar hukumar Borgu a jihar yayin da yaje daukar kudin fansa har miliyan uku.

Kara karanta wannan

Kungiyar Izala ta yi martani kan hallaka malamin musulunci, ta tura sakon gargadi

Rahotannin sun tabbatar da cewa dan bindigan ya mutu ne yayin da ya je daukar kudain fansar har miliyan uku a yankin da ke jihar Neja.

Tsohon gwamnan Yobe ya rasu

Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne a kasar Saudiyya bayan fama da jinya na tsawon lokaci inda aka binne shi a can.

Cikin wadanda suka nuna alhini har da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda ya ce ya rasa babban amini.

Asali: Legit.ng

Online view pixel