Dan Bindiga Ya Mutu Bayan Bindige Shi da Aka Yi Yayin Daukar Kudin Fansa N3m a Jihar Arewa

Dan Bindiga Ya Mutu Bayan Bindige Shi da Aka Yi Yayin Daukar Kudin Fansa N3m a Jihar Arewa

  • Yan sanda sun yi ajalin wani dan bindiga yayin da ya ke daukar kudin fansa har miliyan uku a jihar Neja a jiya Laraba
  • Rundunar ta ce ta yi nasarar bindige dan bindigar a karamar hukumar Borgu a jihar bayan sun yi barazanar sace dan kasuwa
  • Kakakin rundunar ‘ya sanda a jihar, Wasiu Abiodun shi ya bayyana haka a yau Alhamsis 22 ga watan Faburairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Neja – Rundunar ‘yan sanda ta sanar da kisan wani dan bindiga yayin da yaje daukar kudin fansa a jihar Neja.

Rundunar ta ce ta yi nasarar bindige dan bindigar a karamar hukumar Borgu a jihar yayin da yaje daukar kudin fansa har miliyan uku.

Kara karanta wannan

An kai karar Sunusi Lamido ga Tinubu kan bala'in da ke tunkarar Kano kan masarautu, an fadi dalili

Dan bindiga ya hallaka yayin daukar kudin fansa a jihar Arewa
'Yan sanda sun hallaka dan bindiga a jihar Neja. Hoto: NPF, Niger State.
Asali: Facebook

Yadda aka yi nasarar bindige dan bindigar

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar a jihar, Wasiu Abiodun a yau Alhamsis 22 ga watan Faburairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abiodun ya ce wasu ‘yan bindiga sun yi barazanar yin garkuwa da wani fitaccen dan kasuwa a kauyen Bako-Mission, cewar TheCable.

Ya ce ‘yan bindigar sun umarci dan kasuwar ya ajiye musu miliyan uku a wani wuri da ke kauyen Tunga-Umoru.

Martanin 'yan sanda a jihar Neja

Kakkakin rundunar ya ce jami’ansu da ke yankin sun yi arangama da maharan inda suka yi nasarar ceto wani da aka sace, cewar Daily Post.

Sanarwar ta ce:

“A ranar 21 ga watan Faburairu da misalin karfe 10:30 mun samu labarin mahara sun yi barazana ga wani dan kasuwa tare da umartansa ya ajiye musu miliyan uku a wani kauye.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama ‘sojojin bogi’ a Legas, an gano abin da zai faru da su

“Samun bayanin ke da wuya jami’anmu suka bazama aiki inda suka yi arangama da maharan tare da ceto wata mai shekaru 22 ba tare da rauni ba.
“An yi nasarar hallaka daya daga cikinsu a yayin arangamar yayin da muka samu bindiga kirar AK-47.”

Matar aure ta jefo mijinta daga gidan sama

Kun ji cewa wata matar aure ta tunkudo mijinta daga saman bene a jihar Ebonyi yayin da suka samu wata ‘yar hatsaniya.

Marigayin an tabbatar da cewa ya samu matsala da matar ce kan rikicin da suke yi bayan ya auro mata ta biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel