Yajin Aiki: Gwamnan APC Ya Sanya Labule da Shugabannin Kungiyoyin Kwadago, Bayanai Sun Fito

Yajin Aiki: Gwamnan APC Ya Sanya Labule da Shugabannin Kungiyoyin Kwadago, Bayanai Sun Fito

  • Gwamnatin jihar Neja da ƙungiyoyin ƙwadago a jihar sun shiga tattaunawa kan yajin aikin da ƴan ƙwadagon suka fara a jihar
  • Taron dai zai zaƙulo hanyoyin kawo ƙarshen yajin aikin sai baba ta gani da ƙungiyoyin ƙwadagon suka shiga a ranar Laraba, 21 ga watan Fabrairu
  • Manyan jami'an gwamnati da suka haɗa da gwamnan jihar, hugaban majalisar dokoki da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon ke halartar taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Gwamnatin jihar Neja da ƙungiyoyin ƙwadago sun shiga tattaunawa ta sirri kan yajin aikin da ake yi a jihar.

Ɓangarorin biyu na yin tattaunawar ne domin kawo ƙarshen yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadagon suka shiga, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Hukumar DSS ta gargadi kungiyoyin kwadago kan gudanar da zanga-zanga, ta fadi dalili

Gwamna Bago ya gana da kungiyoyin kwadago
Gwamna Bago ya sa labule da shugabannin kungiyoyin kwadago Hoto: @HonBago
Asali: Twitter

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da Gwamna Umaru Bago, shugaban majalisar dokoki, sakataren gwamnatin jiha (SSG), shugaban ma'aikata, kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun haɗa da kwamishinan shari'a, shugaban ƙungiyar ƙwadago da tawagarsa, tare da wasu manyan jami'an gwamnati, rahoton Nigerian Tribune ya tabbatar.

A ranar Laraba ne dai ƙungiyar ƙwadago ta jihar Neja ta sanar da shiga yajin aikin sai baba ta gani wanda zai fara tun saga ranar.

Menene buƙatun ƙungiyoyin ƙwadagon?

Ƙungiyoyin ƙwadagon ta buƙaci gwamnatin jihar da ta sauya duk wasu naɗe-naɗen siyasa a matsayin manyan daraktocin kuɗi, ayyuka da gudanarwa a hukumomi.

Sun kuma buƙaci gwamnati da ta sauya naɗin shugabanni da mambobi da manyan kwamishinoni na hukumar kula da ma'aikata ta ƙananan hukumomi da hukumar ma'aikata da kuma naɗin manyan daraktoci na wasu hukumomi.

Kara karanta wannan

Ana fama da yunwa ƴan bindiga sun ƙona kayan abinci, gidaje da shanu, sun tafka ɓarna a Arewa

Sauran buƙatun sun haɗa da "sahihin bayani daga gwamnati kan biyan ƙarin albashin ma'aikata."

Yajin aikin dai ya fara ne da safiyar Laraba inda aka dakatar da ayyuka a asibitocin gwamnati da makarantu da ofisoshin gwamnati.

Gwamna Bago Zai Ɗauki Ma'aikata

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Umaru Mohammed Bago, zai ɗauki ma'aikatan kiwon lafiya a jihar, sakamakon ƙarancinsu da ake yi a jihar.

Gwamnan ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta ɗauki sabbin ma'aikatan lafiya guda 1,000 tare da maye gurbin waɗanda suka yi ritaya ba tare da ɓata lokaci ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel