Gwamnan APC Ya Kadu Bayan Mutuwar Matan Fitattun Sarakuna 3 a Jiharsa, Ya Tura Sako

Gwamnan APC Ya Kadu Bayan Mutuwar Matan Fitattun Sarakuna 3 a Jiharsa, Ya Tura Sako

  • Abin tausayi ya faru a jihar Imo bayan rasuwar matan sarakuna har guda uku inda Gwamna Hope Uzodinma ya yi jaje
  • Uzodinma ya bayyana mutuwar matan sarakunan a matsayin abin bakin ciki inda ya ce tabbas an samu gibin mai wuyar cikewa
  • Sakataren yada labaran gwamnan, Oguwike Nwachukwu shi ya bayyana haka a yau Talata 5 ga watan Maris a Owerri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Imo – Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya jajantawa fitattun sarakunan gargajiya uku kan rasuwar matansu.

Uzodinma ya bayyana rasuwar matan sarakunan a matsayin babban rashi ga jihar da ma kasar Najeriya baki daya.

Gwamnan APC ya tura sakon jaje bayan mutuwar matan manyan sarakuna 3
Gwamna Uzodinma ya ce tabbas an tafka babban rashi da zai yi wahala a manta. Hoto: Hope Uzodinma.
Asali: Twitter

Wane sako gwamnan ya tura a Imo?

Kara karanta wannan

Ke Butulu Ce, Matar Tsohon Gwamnan APC Ta Soki Surukarta Kan Goyon Bayan Gwamna Mai Ci

Gwamnan ya tura sakon jajen ne ga Mai Martaba Eze Henry Madumere da Eze Sabinus Nwaneche da Eze Reginald Amadi, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda suka mutun sun hada da Ugoeze Marlinda Ulunma da Ugoeze Nkechinyere Nwaneche da kuma Ugoeze Ogechi Amadi.

Henry Madumere shi ne ke sarautar Achi Mbieri a karamar hukumar Mbaitoli da Eze Sabinus Nwaneche da ke sarautar Ahiara Ahiazu.

Sai kuma Mai Martaba Eze Reginald Amadi da ke Obetiti-Nguru da ke karamar hukumar Aboh-Mbaise a jihar Imo.

Wace addu'a gwamnan ya yi ga iyalansu?

Sakataren yada labaran gwamnan, Oguwike Nwachukwu shi ya bayyana haka a yau Talata 5 ga watan Maris a Owerri.

Oguwike ya ce Gwamna Uzodinma ya kadu matuka da mutuwar iyayen mata har guda uku wanda ya ke matukar ganin darajarsu.

Kara karanta wannan

Yayin da 'yan Najeriya ke fama da mahara, harbe-harben sojoji ya hallaka mutum 2 kan wani dalili

A karshe, Uzodinma ya yi addu’ar ubangiji ya bai wa iyalansu hakurin juriya inda ya tura sakon jaje ga iyalan da kuma jihar baki daya.

Har ila yau, Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya yi Allah wadai da harin fasa bututun mai da wasu tsageru suka kai a jihar.

Lamarin ya faru ne a yankin Ohaji na jihar da ke Kudu maso Gabas inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku.

An samu baraka a iyalin Akeredolu

A baya, mun ruwaito cewa uwar gidan marigayi gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ta soki surukarta kan goyon bayan gwamna mai ci.

Betty Akeredolu ta bayyana ‘yar uwar marigayin, Funke Akeredolu Aruna a matsayin butulu kuma ma ci amana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel