Gwamnan APC Ya Yi Magana Mai Zafi Bayan Fashewar Wani Abu Ta Yi Ajalin Rayukan Bayin Allah

Gwamnan APC Ya Yi Magana Mai Zafi Bayan Fashewar Wani Abu Ta Yi Ajalin Rayukan Bayin Allah

  • Gwamna Hope Uzodinma ya yi tir da harin da ya jawo fashewar bututun mai a yankin Ohaji na jihar Imo
  • Ya kuma jajantawa iyalan waɗanda suka mutu a lamarin, inda ya shawarci matasa su guji aikata wannan ɗanyen aiki
  • Uzodinma ya kuma lashi takobin cewa gwamnatinsa ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen kare dukkan bututun da suka ratsa ta jihar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya yi Allah wadai da harin fasa bututun mai da wasu tsagerun barayi suka kai a yankin Ohaji na jihar da ke Kudu maso Gabas.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, fashewar bututun ta yi sanadiyyar mutuwar mutum uku.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya ba da mamaki, ya sake naɗa kwamishinoni huɗu da ya kora daga aiki

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.
Gwamna Uzodinma Ya Yi Magana Bayan Wani Abu Ya Fashe a Imo, Ya Jajantawa Mamata Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Twitter

Gwamna Uzodinma ya nuna damuwarsa da aukuwar lamarin a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Oguwike Nwachuku, ya fitar ranar Jummu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma yi nadamar asarar rayuka da aka yi a sakamakon lamarin, inda ya ce yawaitar fasa bututun mai a yankin abin damuwa ne ga gwamnatin Imo.

Jami’an tsaro sun gano cewa wasu mahara sun yi dirar mikiya a bututun mai a Estate Obitti Rubber Estate, a Ohaji, inda suna tsaka da ɗora kaya a motar da ke aje, kwatsam fashewar ta faru.

Biyar daga cikin barayin da suka yi wannan aika-aika ta haramtacciyar hanya, bayanai sun nuna cewa sun kone ƙurmus ta yadda ba za a iya gane su ba.

Gwamna Uzodinma ya ce jihar ba za ta lamurci shiga cikin tabarbarewar tattalin arziki ba a sakamakon ayyukan baragurbin ɓarayin man fetur.

Kara karanta wannan

'Yan makarantar Ekiti: An bar yaranmu da yunwa sannan ga duka, Iyaye

Uzodinma ya jajantawa iyalan mamatan

Da yake jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan lamari, gwamnan ya shawarci matasan yankin da su guji irin wannan munanan ayyuka.

Ya kuma umarci hukumomin tsaro da su tabbata sun magance matsalar idan kuma ba haka su kawar da ita baki ɗaya, rahoton Vanguard.

Gwamna Uzodimma ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa domin kare bututun mai da suka ratsa ta jihar Imo.

Ƴan bindiga sun sace tawagar amarya

A wani rahoton kuma Miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da gomman mata ƴan kai amarya a jihar Katsina ranar Alhamis da daddare.

Rahotanni daga yankin sun nuna cewa maharan sun sace matan ne bayan sun harbi diraban babbar motar da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262