Gwamnan APC Ya Kori Wasu Hadimai Daga Aiki a Gwamnatinsa, Ya Naɗa Sabbi Nan Take

Gwamnan APC Ya Kori Wasu Hadimai Daga Aiki a Gwamnatinsa, Ya Naɗa Sabbi Nan Take

  • Gwamna Uzodinma na jihar Imo ya ƙara korar wasu hadiman gwamnatinsa yayin da ya sa ƙafa a zangon mulkinsa na biyu
  • Shugaban gwamnonin APC ya kori baki ɗaya jagororin hukumar ISWAMA nan take, sannan kuma ya naɗa sabbin da zasu maye gurbin
  • Hope Uzodinma ya umarci masu barin gado su miƙa harkokin mulkin hukumar hannun waɗanda ya naɗa nan take

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, a ranar Juma’a, 26 ga watan Janairu, ya amince da nadin sabuwar tawagar gudanarwa a hukumar kula da shara ta jihar (ISWAMA).

Sakamakon wannan naɗi da gwamnan ya yi, a yanzu Cyril Njoku ne ya zama sabon shugaban hukumar ISWAMA, kamar yadda The Nation ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamnan arewa ya sassauta dokar zaman gida ta awanni 24 da ya sanya a Mangu, ya faɗi dalili 1

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.
Gwamna Uzodinma Ya Rushe Majalisar Gudanarwa Ta ISWAMA, Ya Nada Sabbi a Imo Hoto: Hope Uzodinma
Asali: Twitter

Bayan haka naɗin sabuwar majalisar gudanawar da Gwamna Uzodinma ya yi ya nuna cewa Mista Ugochukwu Aghazie, shi ne ya zama sabon daraktan ayyuka a hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan naɗe-naɗe na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labarai kuma mai ba gwamna shawara kan harkokin midiya, Oguwike Nwachuku, ya fitar ranar Jumu'a.

Ya kuma bayyana cewa wannan naɗin da aka yi na sabbin waɗanda zasu jagoranci hukumar ISWAMA zai fara aiki ne nan take ba bu ɓata lokaci.

Gwamna Uzodinma ya tsige majalisar gudanarwa ta ISWAMA

Tun da farko, Gwamnan na jam'iyyar APC a shiyyar Kudu maso Gabas ya sallami gaba ɗaya jagororin hukumar kula da ayyukan zubar ta shara ISWAMA daga aiki.

Uzodinma, shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyya mai mulki, ya umarci su miƙa harkokin jagorancin hukumar ga sabbin waɗanda aka naɗa nan take.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba, Sule da wasu gwamnoni 7 da suka shirya zartar da hukuncin kisa kan masu garkuwa

Wannan dai na zuwa ne a daidai loƙacin da Uzodinma ke gyare-gyare a gwamnatinsa bayan karban rantsuwar kama aiki a zangon mulki na biyu.

An sake rantsar da Uzodinma a matsayin gwamnan jihar Imo karo na biyu bayan ya lashe zaɓen gwamnan da aka yi a watan Nuwamba, 2023, rahoton Channels tv.

Rikicin majalisar Ogun ya buɗe sabon shafi

A wani rahoton kuma Tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Ogun, Kunle Oluomo, ya fusata da matakin abokan aikinsa na tsige shi daga kan muƙamin.

Da yake martani kan lamarin ranar Jumu'a a gidansa, Oluomo ya ce yana nan daram a matsayin shugaban majalisar jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel