Bidiyon Zakzaky Yana Magana Kan Harsashi 38 da Likitoci Suka Gano a Kwakwalwarsa Ya Yadu

Bidiyon Zakzaky Yana Magana Kan Harsashi 38 da Likitoci Suka Gano a Kwakwalwarsa Ya Yadu

  • Shugaban kungiyar ‘yan shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya magantu kan jinyar da ya yi, da kuma abun al'ajabin da ya faru a kansa
  • Zakzaky ya bayyana cewa harsasai 38 likitoci suka gano a kansa wadanda suka watsu har zuwa kwakwalwa
  • Haka kuma, Shehin malamin ya ce karfe ya huda kwayar idonsa har aka dinke amma bai daina gani da shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Shugaban kungiyar 'yan uwan Musulmai na Shi'a Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya bayyana wani mu'ujiza da Allah ya nuna a kansa bayan ibtila'in da ya saukar masa.

Zakzaky ya bayyana cewa likitoci sun ga abin mamaki tattare da shi a lokacin da aka kai shi domin yi masa maganin rashin lafiyar da suka same shi.

Kara karanta wannan

Wani uba ya yi watsi da 'yan kai amarya, ya yi wa diyarsa rakiya zuwa dakin mijinta da kansa, bidiyo

Zakzaky ya bayyana yadda Allah ya yi ikonsa a kansa
Bidiyon Zakzaky yana magana kan harasashi 38 da likitoci suka gano a kwakwalwarsa ya yadu Hoto: @am_ghoulam
Asali: Twitter

Malamin addinin ya ce duk da cewar karfe ya ratsa cikin kwayar idanunsa wanda ya kai har sai da aka fito da idanun aka dinke sannan aka mayar masa, Allah bai dauke masa gani da idon ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Likitoci sun ga abun mamaki tattare da ni, Zakzaky

Haka kuma, jagoran 'yan shi'an ya ce a lokacin da za a yi masa aiki a kansa, likitoci sun ci karo da harsasi guda 38 a kansa wadanda suka watsu a zuwa kasan kwakwalwarsa.

A cikin wani bidiyonsa yana jawabi wanda ya yadu a Facebook, Shehin malamin ya ce wani likita ya kasa yarda cewa yana raye saboda wadannan harsasai da suka gano a kansa.

An jiyo Shehin malamin yana cewa:

"Wannan yin Allah ne. Su kansu duk likitocin da suka ga abubuwan da suka faru suna cewa wannan yin Allah ne.

Kara karanta wannan

Hazikin matashi ya kera otal da katafaren gida daga kwalaye, bisararsa ta burge mutane

"Alal misali dangane da idona ko shi likitan wani likita da muka samu a can wani Dr Shu'aibi wani kwararren likitan ido ne, ya ce lallai babu yadda za a yi karfe ya huda ido, mutum ya kuma gani da wannan ido.
"Toh ni kuwa karfe ya huda idon ne aka ciro shi aka dinke kuma Allah ya bar ni da ganina.
"Sannan kuma har wala yau harsasan da ke ka, akwai wani likita da ya gani ihu ma ya yi yace babu yadda za a yi wannan mutumin ma ya zama yana da rai, yanzu haka ana nufin wannan yana da rai?
"Harsashi kuci-kuci har guda 38 a kai sun watsu wasu har karkashin kwakwalwa, toh muna iya cewa Allah mai rayawa shine ya raya, shi ya yi halitta kuma shine ya raya."

Kalli bidiyon a kasa:

'Yan shi'a sun yi tattaki a Abuja

A wani labarin, mun ji cewa 'yan shi'a ƙarƙashin kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) sun bayyana goyon baya ga Falasdinawa biyo bayan sake ɓarkewar rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

Ana alaƙanta sabon yaƙin da ya ɓarke da farmakin da aka kai Masallaci Al-Aqsa da kuma sansanin 'yan gudun hijira da ke Gaza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel