Gasar AFCON: An Shiga Karancin Rigunan Super Eagles a Kano, ’Yan Kwasuwa Sun Kwashi Ganima

Gasar AFCON: An Shiga Karancin Rigunan Super Eagles a Kano, ’Yan Kwasuwa Sun Kwashi Ganima

  • Kanawa masu kishin kasa sun shiga damuwa bayan dumfarowar karancin rigunan kwallo na Super Eagles
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Najeriya ke fatan lallasa kishiyarta a wasan karshe na AFCON da ake yi
  • 'Yan Najeriya na ci gaba da sa rai, ana kyautata zaton su dauki kofin na nahiyar Afrika mai cike da tarihi

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Kano - 'Yan Najeriya masu kishin kasa a jihar Kano sun shiga rudani yayin da rigunan kungiyar Super Eagles suka kare kaf a kasuwa gabanin wasan karshe na AFCON.

A rahoton da muke samu daga jihar, a halin yanzu wasu 'yan jihar na neman siyan rigar ruwa a jallo, amma hakan ya ci tura duba da yadda ta yi karanci a kasuwannin Kano.

Kara karanta wannan

AFCON: Ana saura kwana 4 aurensa ya rasu, cewar iyalan marigayi Ayuba a Kwara, bayanai sun fito

Ya zuwa jiya Asabar 10 ga watan Faburairu, rigar da ake siyarwa N5000 ta koma N15,000 nan take baya ga wahalar samunta.

'Yan Kano sun rasa inda za su jesin Najeriya
Rigar Super Eagles ta kare a Kano, Kanawa sun shiga jimami da kunci | Hoto: MB Media
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nawa ne rigar Super Eagles a Kano?

Da yake magana kan halin da ake ciki, wani dan kishin kasa Usman Muhammad ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa:

"Yanzu da nake magana, na gaza samun rigar a Kano. Wani ya hada ni da abokinsa a Kaduna don a samo min.
"Haka sai da muka yi ciniki kafin a samu min amma mai siyarwan ya ce, ana siyarwa N20,000 ko N25,000 a Kaduna. Yanzu haka, ina jiran a kawo min nawa ne kafin karfe 5 na yamma."

Ana samun rigar Super Eagles a Kano?

A nasa bangaren, wani matashi Junior Lukas ya bayyana kokensa kan rasa rigar 'yan wasan da zai sanya duk da cewa a shirye yake ya siya da tsada.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnatin Kano ta cika alkawari, ta dira kan rumbun ajiyar masu boye abinci

Da yake magana, ya ce:

"Gaskiya na so a ce na samu amma tun da babu, ya na iya duk da kuwa zan iya siya ko da N10,000 ne."

Legit Hausa ta tattaro cewa, karancin rigunan ya samo asali ne da yadda 'yan kasuwa suka boye ta da burin cin riba mai yawa a daidai lokacin wasannin AFCON.

Idan baku manta ba, a daren yau Lahadi ne Super Eagles ke shirin buga wasar karshe da kasar Ivory Coast a wasan karshe na AFCON da aka kwana biyu ana bugawa.

Su wa za su lashe kofin gasar AFCON?

A bangare guda, shahararren Fasto, Dakta Kan Ebube Muonso yi hasashen kasar da za ta lashe wasan AFCON da aka zo karshensa a yau Lahadi.

Ya bayyana yadda ya hango nasarar tare da nuna dalilan da ya dogara da su a wasannin da aka buga gaba daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel