AFCON: Mourinho Ya Fadi Kasar da Ya Ke So Ta Lashe Gasar, Ya Tura Sako Ga Abokinsa, Peseiro

AFCON: Mourinho Ya Fadi Kasar da Ya Ke So Ta Lashe Gasar, Ya Tura Sako Ga Abokinsa, Peseiro

  • Jose Mourinho, tsohon kocin Manchester United ya bayyana kasar da ya ke so ta ci gasar AFCON da za a yi a yau Lahadi
  • Mourinho ya ce ya na muradin tawagar Super Eagles ta lashe wasan karshen da za a gudanar a daren yau da Ivory Coast
  • Wannan na zuwa ne yayin da Najeriya za ta kara da Ivory Coast a daren yau Lahadi 11 ga watan Faburairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Tsohon kocin Chelsea da Mancheser United, Jose Mourinho ya bayyana kasar da ya ke so ta lashe gasar AFCON.

Mourinho ya ce ya na muradin tawagar Super Eagles ta lashe wasan karshen da za a gudanar a daren yau da mai masaukin baki, Ivory Coast.

Kara karanta wannan

Gasar AFCON: An shiga karancin rigunan Super Eagles a Kano, 'yan kwasuwa sun kwashi ganima

Mourinho ya fadi kasar da ya ke so ta lashe gasar AFCON
Mourinho ya nuna goyon baya ga tawagar Super Eagles. Hoto: @josemourinho, @ng_supereagles.
Asali: Instagram

Mene Mourinho ke cewa kan wasan Najeriya?

Kocin ya bayyana haka ne a yau Lahadi 11 ga watan Faburairu yayin hira da FIVE UK inda ya ce kocin Najeriya babban abokinsa ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ya ke magana kan wasan a yau, Mourinho ya na so Super Eagles kocinta, Jose Peseiro su yi nasara.

A cewarsa:

“Mun taso da Peseiro inda muka hadu a Jami’a kullum muna tare na tsawon shekaru biyar.
“Babban abokina a wasan kwallon kafa yau zai buga wasan karshe, kocin Najeriya babban abokina ne mun taso tare.
“Mun yi karatu tare, mun je Jami’a tare, mun shafe shekaru biyar tare kuma mun bar Jami’a a lokaci daya, shi ne babban abokina a kwallon kafa, kuma yanzu ya samu daman kafa tarihi, kocin Portugal bai taba cin kofin AFCON ba.”

Kara karanta wannan

AFCON: Ahmed Musa ya yi magana kan makomarsa bayan kammala gasar, ya bai wa jama'a mamaki

Hirar da aka yi da Mourinho

Wannan na zuwa ne yayin da Najeriya za ta kara da Ivory Coast a daren yau Lahadi 11 ga watan Faburairu da misalin karfe tara na dare.

Musa ya yi magana kan makomarsa

Kun ji cewa Kyaftin din tawagar Super Eagles, Ahmed Musa ya ce ba ya tsammanin barin kungiyar nan kusa.

Musa wanda ke neman cin kofin AFCON a karo na biyu bai taba buga ko da wasa daya ba a wannan gasa da ake yi a Ivory Coast.

Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel