Babban Jigon APC Ya Yanke Jiki Ya Mutu Yayin da Ya Ke Kallon Wasan Najeriya

Babban Jigon APC Ya Yanke Jiki Ya Mutu Yayin da Ya Ke Kallon Wasan Najeriya

  • Jigon jam'iyyar APC kuma tsohon dan majalisar wakilai, Cairo Ojougboh, ya yanke jiki ya mutu yayin da yake kallon wasan Najeriya da Arika ta Kudu
  • An ce Ojougboh ya fadi ne a lokacin da kasar Afrika ta Kudu ta samu bugun fenariti kan 'yan Super Eagles a wasan kusa da karshe na AFCON 2023
  • Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi alhinin mutuwar farat daya da dan siyasar na Delta ya yi

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da

Wani jigon jam'iyyar APC kuma tsohon dan majalisar wakjilai, wanda ya wakilci mazabar Ika ta jihar Delta a majalisar tarayya, Cairo Ojougboh, ya mutu.

Ojougboh, wanda ya shahara saboda rashin tsoron fitowa ya yi magana ya kwanta dama ne a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, yayin da yake kallon wasan Najeriya da Afrika ta Kudu a gasar AFCON da ke gudana.

Kara karanta wannan

AFCON: Matashi mai bautar kasa ya rasa ransa a jihar Arewa kan wasan Najeriya, bayanai sun fito

Jigon APC, Cairo Ojougboh ya kwanta dama
Babban Jigon APC Ya Yanke Jiki Ya Mutu Yayin da Ya Ke Kallon Wasan Najeriya Hoto: Cairo Ojougboh
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito daga majiya mai tushe cewa dan siyasar ya mutu ne a yayin da ake buga wasan fenariti a ragar Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce:

"Ya yanke jiki ya fadi a lokacin da aka bayar da fenariti akan Najeriyan yayin gasar AFCON da Kudu ta Afrika a wasan kusa da karshe da aka yi a ranar Laraba a Bouake, Ivory Coast."

Ojougboh, wanda tsohon daraktan ayyuka ne na kwamitin riko na hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC), na daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC da aka kora daga jam’iyyar bisa zargin cin dunduniyar jam’iyyar a zaben 2023.

Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Ika ta Kudu a jihar, Hilary Ibude, ne ya sanya hannu a takardar korar mai kwanan wata 27 ga watan Maris.

Ibude ya bayyana cewa an kori marigayi Ojougboh daga jam'iyyar bayan korafe-korafen da aka shigar a kansa a cikin abin da ya ce yana da nasaba da tsaikon da jam'iyyar ta samu a zaben.

Kara karanta wannan

AFCON 2023: Shettima ya taya 'yan Super Eagles murna bayan lallasa Afrika ta Kudu, bidiyon ya yadu

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi alhinin rashin a dandalinsa na soshiyal midiya inda ya bayyana marigayin a matsayin abokinsa kuma mai kishin kasa.

Ya rubuta a shafin nasa:

"Mutuwar farat daya da abokina Dr. Cairo Ojougboh ya yi ya sanya ni bakin ciki. Kaunarsa ga kasarmu na da yawa."

Lauya ya zanke jiki ya fadi a kotu

A wani mun ji cewa ajali ya riski wani lauya a ƙofar shiga harabar kotu a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, lauyan ya yanke jiki ya faɗi kuma ya sume nan take, domin bayanai sun nuna ya fita a hayyacinsa a kofar shiga kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel