Chile: Tsohon Shugaban Ƙasa Ya Mutu a Mummunan Hatsarin Jirgin Sama, Bayanai Sun Fito

Chile: Tsohon Shugaban Ƙasa Ya Mutu a Mummunan Hatsarin Jirgin Sama, Bayanai Sun Fito

  • Tsohon shugaban kasar Chile, Sebastian Pinera, wanda ya yi zango biyu a karagar mulki, ya mutu a hatsarin jirgin sama yana da shekaru 74
  • Sauran mutum uku da ke tare da shi a cikin jirgin helikwafta sun tsallake rijiya da baya yayin da jirgin ya rikito a wani tafki
  • Legit Hausa ta fahimci cewa an gano gawar marigayin a wurin da hatsarin ya afku da ke kusa da kudancin garin Lago Ranco

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Santiago, Chile - Tsohon shugaban ƙasar Chile, Sebastian Pinera, ya mutu a hatsarin jirgin helikwafta da ya rutsa da shi.

Jirgin mai saukar angulu wanda ya ɗauko tsohon shugaban kasar ya gamu da haɗari ne a yankin Los Rios da ke kudancin ƙasar Chile.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da gobara ta kashe yaro dan shekara 4 a Jihar Kano

Tsohon shugaban ƙasar Chile, Sabastian Pinera ya mutu.
Tsohon Shugaban Kasar Chile, Sebastian Pinera, Ya Mutu a Hatsarin Jirgin Sama Hoto: Agencia Makro
Asali: Getty Images

Ofishin marigayi Pinera, sanannen ɗan kasuwa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 6 ga watan Fabrairu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Reuters, ministan cikin gida, Carolina Toha, ya tabbatar da mutuwar tsohon shugaban ƙasar ɗan shekara 74 wanda ya mulki Chile daga 2010-2014 da 2018-2022.

An fara ta'aziyyar rasuwar Pinera

Da take alhinin rasuwar jagoran, tsohuwar sakataren lafiya a Chile, Paula Daza, ta wallafa a shafinta na X cewa:

"A yau, mun rasa babban shugaban kasar Chile, jagora kuma gogagge. A taƙaice dai shugaba Sebastian Pinera abun kwatance ne, jagora da mai ba da shawara.
"A yau, ina mika gaisuwata ta musamman da ta'aziyya ga iyalansa, wadanda nake girmamawa."

Yaushe ya mulki ƙasar Chile?

Legit Hausa ta tattaro cewa marigayi Pinera ya mulki ƙasar Chile a tsaƙanin shekarar 2010 zuwa 2014, daga bisani kuma ya sake dawowa zango na biyu daga 2018 zuwa 2022.

Kara karanta wannan

Kogi: Yan bindiga sun sace fasinjojin wasu manyan motoci guda biyu a hanyar zuwa Abuja

A lokacin da jirginsa ya yi hatsari, an ce an yi ta ruwan sama babu kaƙƙautawa a yankin.

Sai dai babu tabbacin ko yanayin na ruwan sama ne ya haddasa haɗarin jirgin da tsohon shugaban ke ciki, cewar rahoton CNN.

Farfesan ABU ya kwanta dama

A wani rahoton kuma Allah ya karbi rayuwar fitaccen Farfesa, Yusuf Dankofa a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kaduna.

Marigayin ya rasu da safiyar yau Talata 6 ga watan Fabrairu a Kaduna ya na da shekaru 61 a duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel