Tashin Hankali Yayin da Wani Lauya Ya Yanke Jiki Ya Faɗi a Kofar Kotu, Allah Ya Masa Rasuwa

Tashin Hankali Yayin da Wani Lauya Ya Yanke Jiki Ya Faɗi a Kofar Kotu, Allah Ya Masa Rasuwa

  • Allah ya yi wani lauya masanin doka rasuwa a kofar shigar harabar kotun majistire a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas
  • Lauya mai suna, Eze Agala, ya yanke jiki ya faɗi ne bayan ya fito daga cikin kotun kuma likitoci sun tabbatar da rai ya yi halinsa a asibiti
  • Har kawo yanzun babu wata sanarwa a hukumance daga kungiyar lauyoyi NBA reshen jihar ko kuma rundunar ƴan sanda

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Rahotanni sun nuna cewa ajali ya riski wani lauya a ƙofar shiga harabar kotu a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, lauyan ya yanke jiki ya faɗi kuma ya sume nan take, domin bayanai sun nuna ya fita a hayyacinsa a kofar shiga kotu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da yawa sun mutu yayin da suka kai farmaki kan jami'an tsaro a jihar Arewa, an kashe sojoji

Lauya ya gamu da ajalinsa a kofar shiga kotu.
Lauya Ya Yanke Jiki Ya Faɗi a Kofar Shiga Kotu, Allah Ya Masa Rasuwa a Fatakwal Hoto: Channelstv
Asali: Twitter

An gano cewa lauyan mai suna, Eze Agala, ɗan asalin garin Ibaa da ke ƙaramar hukumar Emohua a jihar Ribas ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masanin dokar ya faɗi sumamme ne jim kaɗan bayan ya sa ƙafa ya fito daga harabar ginin Kotun Majistire da ke titin Moscow a Fatakwal.

Allah ya yi wa lauyan rasuwa bayan kai shi asibiti

Bugu da ƙari, jama'ar da ke wurin sun gaggauta kai shi asibitin rundunar ƴan sanda inda likitoci suka tabbatar da cewa rai ya yi halinsa.

Sai dai har kawo yanzu shugabannin ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen jihar Ribas ba su fitar da sanarwa a hukumance kan abin da ya faru da mamban na su ba.

Amma wani lauya a jihar mai arzikin man fetur, Felix Ashimole, ya fito ya tabbatar da faruwar lamarin a kafafen sada zumunta, Sahara Reporters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tono tushen matsalar ƴan bindiga a Arewa, ya jero hanyoyin magance su

Mista Felix ya riƙa tura sakon yadda abokin aikinsa ya yanke jiki ya faɗi matacce a gaban kotu a kafar sada zumunta Whatsapp da wasu wuraren daban.

Tsohon shugaban ƙasa ya mutu a haɗarin jirgi

A wani rahoton kun ji cewa Tsohon shugaban kasar Chile, Sebastian Pinera, wanda ya yi zango biyu a karagar mulki, ya mutu a hatsarin jirgin sama yana da shekaru 74.

Sauran mutum uku da ke tare da shi a cikin jirgin helikwafta sun tsallake rijiya da baya yayin da jirgin ya rikito a wani tafki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel