AFCON 2023: Shettima Ya Taya ‘Yan Super Eagles Murna Bayan Lallasa Afrika Ta Kudu, Bidiyon Ya Yadu

AFCON 2023: Shettima Ya Taya ‘Yan Super Eagles Murna Bayan Lallasa Afrika Ta Kudu, Bidiyon Ya Yadu

  • Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya kasance a Cote d’Ivoire a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, domin karfafawa 'yan wasan Super Eagles kafa a gasar AFCON na 2023
  • An hango Shettima a tsaye inda ya zauna kusa da Patrice Motsepe, shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF)
  • Bayan nasarar da Najeriya ta samu, Shettima ya taya 'yan Super Eagles murna a filin wasa yayin da 'yan wasan ke taka rawa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima, ya shiga sahun 'yan wasan Super Eagles wajen murna bayan nasarar da suka samu kan Afrika ta Kudu a gasar cin kofin Afrika (AFCON) a ranar Laraba 7 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

AFCON: Kada ka kuskura ka dawo kasarmu, 'yan Afirka ta Kudu sun gargadi dan Najeriya, sun yi bayani

Jaridar Legit ta rahoto cewa Shettima na cikin manyan mutanen da suka kalli wasan 'yan Eagles a filin wasa na Stade de la Paix dake Bouaké.

Shettima ya taya 'yan Eagles murna
AFCON 2023: Shettima Ya Taya ‘Yan Super Eagles Murna Bayan Lallasa Afrika Ta Kudu, Bidiyon Ya Yadu Hoto: Anadolu, Ken Ishii
Asali: Getty Images

Najeriya ta kai wasan karshe a gasar AFCON 2023 bayan da ta buga wasan kusa da na karshe da Afirka ta Kudu wadda ta yi zarra.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ne karo na farko da Super Eagles ke kaiwa karshen gasar AFCON tun a 2013 lokacin da suka lallasa Burkina Faso da 1-0 wanda Sunday Mba ya yi nasarar zura kwallo a raga.

A yayin da suke neman matsayinsu na hudu, 'yan siyasa da wasu fitattun mutane sun yi tattaki zuwa kasar Ivory Coast domin marawa kasarsu baya.

Daga cikin wadanda suka isa kasar Ivory Coast harda Shettima - a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Babban jigon APC ya yanke jiki ya mutu yayin da ya ke kallon wasan Najeriya

Haka kuma, ba a bar Shettima a baya ba wajen shiga sahun masu murna a filin wasan bayan nasarar da Najeriya ta samu.

Jaridar Legit ta ahimci cewa mataimakin shugaban kasa na Najeriya ya kuma hadu da 'yan wasan Eagles a dakin shiryawansu.

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, sunan Shettima na tashi a dandalin x (wanda aka fi sani da Twitter a baya).

Kalli bidiyon Shettima a filin wasa yana taya 'yan Eagles murna a kasa:

Yadda Najeriya ta fara cin Afrika ta Kudu

A baya mun ji cewa Kaftin din Najeriya, William Troost-Ekong, ya zura kwallo ta farko a ragar Afrika ta Kudu bayan da Najeriya ta samu bugun finareti.

Kuskuren da Samuel Chkuweeze ya yi a yayin da suka yi karo da Osimhen ya kai ga bugun fanaretin. Read more: https://hausa.legit.ng/wasanni/1577614-afcon-2023-najeriya-ta-zura-kwallon-farko-a-ragar-afrika-ta-kudu/

Asali: Legit.ng

Online view pixel