Labari Mai Dadi: Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Legas Ya Shaki Iskar 'Yanci

Labari Mai Dadi: Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Legas Ya Shaki Iskar 'Yanci

  • Masu garkuwa da mutanen da suka sace shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Legas a titin Legas-Ibadan sun sako shi
  • Philip Aivoji, ya shaki iskar 'yanci ne a ranar Litinin, 29 ga watan Janairu, bayan ya shafe kwanaki hudu a hannun 'yan bindigar da suka sace shi
  • Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da sakin nasa, amma ba a sanar da ko an biya kudin fansa kafin suka sake shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Legas, Philip Aivoji, wanda wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene kowanene ba suka sace shi, ya shaki iskar yanci.

An sako Aivoji ne kwanaki hudu bayan an yi garkuwa da shi a babban titin Legas zuwa Ibadan, jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An shiga dar-dar bayan mahara sun sace 'yan sanda 3 a bakin aiki da ke kare jama'a, bayanai sun fito

Shugaban PDP reshen Legas ya shaki iskar 'yanci
Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Legas Ya Shaki Iskar 'Yanci Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

An yi garkuwa da Aivoji tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar a yankin Ogere, da ke titin Legas zuwa Ibadan a ranar Alhamis, yayin da suke dawowa daga taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ne ya kira taron, wanda aka gudanar a garin Ibadan, babban birnin jihar.

Sakataren labarai na jihar, Hakeem Amode ne yasanar da batun sakin nasa a wata ‘yar gajeriyar sanarwa da ya fitar da misalin karfe 1:15 na safiyar ranar Litinin, 29 ga watan Janairu.

Jaridar The Cable ta nakalto Amode yana cewa:

"Masu garkuwa da mutane sun sako shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Legas.
“Daga karshe Hon Philip Olabode Aivoji shugaban PDP reshen jihar Legas ya samu 'yanci bayan shafe kwanaki 4 a sansanin masu garkuwa da mutane."
"Muna amfani da wannan damar don nuna godiya ga addu'o'inku saboda rahamar Allah ya bayyana karara."

Kara karanta wannan

Kudin Fansa: Masu garkuwa suna barazanar hallaka mutanen Abuja 11 da aka sace

"Muna godaiya da kulawa da addu'o'in ku."

Rundunar 'yan sanda ta yi martani

A halin da ake ciki, kwamishinan 'yan sandan jihar Ogun, Abiodun Alamutu, ma ya tabbatar da da sakin Aivoji, a safiyar yau Litinin.

Da yake zantawa da jaridar Punch, Alamutu ya ce:

"Eh, an sako shi a safiyar yau, amma ba ni da labarin biyan kudin fansa.”

'Yan sanda sun fafata da 'yan bindiga

A baya mun ji cewa Bilikisu Kazeem, wata mata mai shekaru 37 ta mutu sakamakon harbin da ya same ta yayin da ake musayar wuta tsakanin 'yan sanda da wadanda suka yi garkuwa da shugaban PDP na Legas.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu, kakakin rundunar yan sandan Ogun, Omolola Odutola, ne ya bayyana hakan a Abeokuta, babban birnin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel