Abu Ya Girma: Jam'iyyar APC Ta Yi Magana Kan Tsohon Gwamnan Arewa da Ke Son Tsige Ganduje

Abu Ya Girma: Jam'iyyar APC Ta Yi Magana Kan Tsohon Gwamnan Arewa da Ke Son Tsige Ganduje

  • Jam'iyyar APC ya aike da saƙo ga tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, kan alamun da suka nuna yana son karɓe shugabancin APC
  • A ranar Litinin aka ga wasu fastocin Yahaya Bello a wasu sassan Abuja waɗanda suka nuna yana sha'awar kujerar Ganduje
  • Amma sakataren watsa labaran APC na ƙasa, Felix Morka, ya ce babu gurɓi ko kankani a sakateriyar jam'iyya mai mulki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta maida martani kan fastocin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da suka mamaye Abuja.

A jiya Litinin ne aka ga fastocin tsohon gwamnan a wasu sassan Abuja, waɗanda ke nuni da yana sha'awar kujerar shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka halaka shugabannin matasa 2 a jihar PDP

Tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Ganduje: "Babu wuri a gidan Buhari" Jam'iyyar APC ta maida martani ga Yahaya Bello Hoto: OfficialAPCNig
Asali: Twitter

Rahoton Vanguard ya tattaro cewa ana raɗe-raɗin cewa wasu manyan Arewa ta Tsakiya na gunagunin kwace kujerar shugaban APC daga yankinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ya biyo bayan tilastawa tsohon gwamnan Nasarawa (Arewa ta Tsakiya), Abdulahi Adamu, murabus daga muƙamin.

Sai dai jim kaɗan bayan haka ne aka maye gurbinsa da tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, daga shiyyar Arewa maso Yamma.

APC ta aike da saƙo ga Yahaya Bello

Da yake tsokaci kan lamarin, sakataren watsa labaran APC, Felix Morka, ya buƙaci Bello ya kyale kwamitin gudanarwa karkashin Abdullahi Ganduje ya yi aikinsa.

Duk da Bello bai fito ya nuna sha'awarsa a hukumance ba, kakakin APC ya ce babu gurɓi ko kwayar zarra a sakateriyar jam'iyya mai mulki ta ƙasa.

Ya kuma jaddada mubaya'ar kwamitin gudanarwa NWC ga Dakta Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

ShIn da gaske Yahaya Bello na neman kujerar Ganduje a APC? Gaskiya ta bayyana

Felix Morka ya gargadi tsohon gwamnan Kogi da ya daina haifar da ruɗani a jam’iyyar, yana mai cewa akwai mai riƙe da matsayin shugaban jam’iyyar na kasa a yanzu.

Morka ya yi wannan gargadin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar ta kasa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Radda ya tallafawa wɗaanda aka ceto daga masu garkuwa

A wani rahoton kuma Gwamna Dikko Radda ya tallafawa mutane 35 da aka ceto daga hannun ƴan bindiga domin su farfaɗo da kasuwancinsu.

Malam Dikko na jihar Katsina ya bai wa kowane ɗaya daga cikin mutanen tallafin N100,000 yayin da ya karɓe su daga hannun sojoji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel