Dakarun Sojoji Sun Sheke Yan Ta'adda 10 Tare da Cafke Ƙasurgumin Shugaban Yan Bindiga

Dakarun Sojoji Sun Sheke Yan Ta'adda 10 Tare da Cafke Ƙasurgumin Shugaban Yan Bindiga

  • Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun samu nasarar sheƙe ƴan ta'adda 10 a yankin Arewa maso Yamma
  • Sojojin ma rundunar Operation Hadarin Daji sun kuma cafke wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga a Zamfara
  • A yayin samamen da sojojin suka kai, sun kuma samu nasarar cafƙe masu safarar makamai tare da ƙwace alburusai masu yawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Rundunar sojin Najeriya ta sanar da kashe ƴan ta'adda 10 tare da cafke wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.

Hakazalika, sojojin sun kame masu safarar makamai tare da ƙwace alburusai yayin samame a jihohin Zamfara, Kebbi, Sokoto, da Katsina, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: An kashe manyan ƴan bindiga 3 yayin musayar wuta a dajin iyakar Abuja da Kaduna

Sojoji sun sheke yan ta'adda
Sojoji sun sheke yan ta'adda 10 a yankin Arewa maso Yamma Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Jami’in yaɗa labarai na rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadarin Daji, Kyaftin Yagata Ibrahim, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Asabar, a birnin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace irin nasara sojojin suka samu?

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"A wani samame na baya-bayan nan da rundunar ta kai a ranar 26 ga watan Janairu, sojojin sun yi nasarar fatattakar ƴan ta’adda a ƙauyukan Pada, Matso-Matso da Yurlumu da ke ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina.
"A yayin farmakin an kashe ƴan ta’adda bakwai yayin da wasu suka tsere da munanan raunukan harbin bindiga.
"A wannan rana, sojojin OPHD a Zamfara da ke sintiri a yaƙin da suke yi sun kashe ƴan ta’adda biyu a ƙauyukan Getso da Ubaka da ke ƙarƙashin karamar hukumar Maru.
"Sojojin sun kwato bindiga ƙirar AK47 guda daya, jigida ɗaya da harsashi na musamman mai kaurin 7.62mm da kuma babura guda biyu."

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji yan ta'adda sun ceto mutanen da suka sace a Kebbi

Ya ci gaba da cewa sojojin sun mayar da martani kan wani rahoton sirri da aka samu kan zirga-zirgar ƴan ta’addan a kan hanyar Sheme-Dandume a Jihar Katsina, inda suka yi artabu da ƴan ta’addan, sannan suka kashe ɗaya, tare da tilastawa wasu tserewa.

Sojoji sun cafke shugaban ƴan ta'adda

Rundunar Sojin ta kuma bayar da rahoton kama Usman Abubakar, wanda aka fi sani da Harinde, wani fitaccen shugaban ƴan bindiga a Zamfara, a ranar 26 ga watan Janairu, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Abubakar, mai shekaru 35, ya daɗe yana aikata ta’addanci a ƙananan hukumomin Shinkafi da Zurmi da sauran ƙauyukan jihar Sokoto.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin jihar Katsina, mai suna Kabir Ibrahim, wanda ya yaba da wannan namijin ƙoƙarin da dakarun sojojin suka yi.

Ya bayyana cewa nasarar da suka samu abun a yaba ce, inda ya yi addu'ar Allah ya ƙara musu ƙarfin gwiwar ci gaba da ƙoƙarin da suke wajen kawo ƙarshen ƴan ta'adda.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace mata da miji da yaransu a Kaduna

A cewarsa:

"Sojojin sun yi ƙoƙari sosai kuma abin da suka yi abun a yaba ne, muna addu'ar Allah ya ci gaba da ba su nasara kan miyagu."

Ƴan Ta'adda Sun Nemi Maƙudan Kuɗin Fansa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan da suka sace wasu mutum 31 a jihar Katsina sun faɗi kuɗin fansan da suke so a ba su.

Miyagun ƴan ta'addan dai sun buƙaci a ba su N30m kafin su bar mutanen su shaƙi iskar ƴanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel