Hukumar JAMB ta Saki Wasu Sakamakon Jarrabawar UTME da ta Rike a 2024

Hukumar JAMB ta Saki Wasu Sakamakon Jarrabawar UTME da ta Rike a 2024

  • Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB ta saki wasu daga sakamakon jarrabawar da ta rike a baya bisa zargin laifuka daban-daban
  • An saki karin sakamakon jarrabawar dalibai 531 da ake kara duba a kansu bisa zargin satar jarrabawa da sauran laifukan da suka sabawa rubuta jarrabawar
  • JAMB ta ce tana zurfafa bincike kan sakamakon kusan dalibai 64,000, kuma ana ci gaba da bincike kan wasu daliban domin tabbatar da sahihancin sakamakon

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB ta saki sakamakon dalibai 531 da ta rike a baya.

Dalibai 64,624 ne hukumar ta ki sakin sakamakon jarrabawar UTME da suka rubuta saboda zargin aikata ba daidai ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fadi dalilin fara rajistar gawan da ake birnewa a makabartu

Daliban JAMB
Hukumar JAMB ta saki sakamakon dalibai 531 Hoto: Joint Admission and Matriculation Board
Asali: Facebook

Hukumar ta ce tana bincike kan jarrabawar domin tabbatar da sahihancinsa kafin a sake sakamakon, kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

JAMB na binciken sakamakon UTME 64,000

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta ce tana zurfafa bincike kan sakamakon dalibai 64, 000 da ta rike sakamakon zarge-zargen aikata ba dai-dai ba.

Amma a yanzu an saki sakamakon 531 daga ciki wanda ya kawo jummalar sakamakon dalibai 1,842,897 da aka saki.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Fabian Benjamin ya sanyawa hannu, inda ya kara da cewa an gano wadanda suka aikata laifuka 81 zuwa yanzu, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

Ya kara da cewa har yanzu suna duba kan batun daliban da suka yi sojan gona wajen rubutawa wasu jarrabawar.

Hukumar ta kuma musanta labarin cewa an samu wanda ya samu sakamakon UTME ba tare da rubuta jarrabawar ba.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta dawo da lantarki a garuruwan da aka yi shekaru babu wuta a Sokoto

An hana masu hijabi jarrabawar JAMB?

Kun ji a baya cewa Yusuf Nuraddeen, wani lauya mazaunin jihar Lagos ya bayyana muzgunawa mata masu sanya hijabi da wasu cibiyoyin JAMB ke yi a matsayin ta’addanci.

Ya tunatar da gwamnati muhimmancin daukar mataki da hukunta dukkan wadanda aka kama suna hana matan rubuta jarrabawa ko ci musu mutunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel