Dakarun Sojoji Sun Ragargaji Yan Ta'adda, Sun Ceto Mutanen da Suka Sace a Kebbi

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji Yan Ta'adda, Sun Ceto Mutanen da Suka Sace a Kebbi

  • Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan miyagun ƴan ta'adda da ke addabar bayin Allah a jihar Kebbi
  • Dakarun sojojin tare da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro da ƴan banga sun kai samame a maɓoyar ƴan ta'adda da ke ƙaramar hukumar Shanga ta jihar
  • A yayin samamen da sojojin suka kai a maɓoyar ƴan ta'addan, sun samu nasarar sheƙe ɗan ta'adda ɗaya tare da ceto mutum huɗu da aka yi garkuwa da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Dakarun runduna ta takwas ta sojojin Najeriya tare da jami’an tsaron farin kaya da na sibil difens da ƴan banga a safiyar ranar Talata sun kai farmaki kan wani sansanin ƴan ta’adda a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace mata da miji da yaransu a Kaduna

Sojojin, a yayin samamen sun kashe ɗaya daga cikin ƴan ta’addan, tare da kuɓutar da mutum huɗu da aka yi garkuwa da su, tare da ƙwato makamai da alburusai.

Sojoji sun ragargaji yan ta'adda a Kebbi
Dakarun sojoji sun ragargaji yan ta'adda a Kebbi Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar soji ta ɗaya da ke Gusau, kyaftin Yahya Ibrahim ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojojin suka kai samamen

A kalamansa:

"An kai samamen ne a maboyar ƴan ta’addan da ke ƙauyen Sabon Gari da ke ƙaramar hukumar Shanga a Jihar Kebbi.
"A yayin farmakin, sojoji sun kashe ɗaya daga cikin ƴan ta’addan tare da ceto mutum huɗu da aka yi garkuwa da su.
"Sojojin sun kuma ƙwato bindigu ƙirar AK-47 guda uku, jigida guda uku, harsashi na musamman guda 142 masu kaurin 7.62mm da kayan sojoji guda biyu."

Ya ƙara da cewa dukkan mutanen da aka ceto an haɗa su da iyalansu, yayin da sojoji ke ci gaba da bin diddigin ƴan ta'addan da suka tsere.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta lakume kayayyakin miliyoyin naira a fitacciyar kasuwar jihar Arewa

Sojoji Sun Sheƙe Shugaban Ƴan Ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojin sama sun sheƙe wani ƙasurgumin shugaban ƴan ta'adda a jihar Kaduna.

Sojojin sun sheƙe ƙasurgumin ɗan ta'addan ne tare da mayaƙansa a wani hari ta sama da a kai a maɓoyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel