Uba Sani Ya Fara Shirin Tashin Makarantu Sama da 300 a Wasu Yankuna a Kaduna

Uba Sani Ya Fara Shirin Tashin Makarantu Sama da 300 a Wasu Yankuna a Kaduna

  • Gwamnatin Kaduna karkashin Malam Uba Sani ta fara shirin haɗe makarantu 359 da waɗanda ke garuruwa masu aminci a faɗin jihar
  • Gwamna Uba Sani ya ce hakan na ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin ke ɗauka domin kare makarantu, ɗalibai da malamai daga harin ƴan bindiga
  • Shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, Sani Kila ya koka kan yadda aka samu raguwar shiga makaranta a jihar saboda fargaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Gwamnatin Kaduna ta bayyana shirin hade makarantu 359 saboda yawaitar hare-haren ƴan bindiga wanda ke haddasa yawan garkuwa da ɗalibai.

Gwamna Uba Sani ya bayyana haka a wurin taron masu ruwa da tsaki da kuma horar da rundunar tsaron makarantu a Kaduna, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya faɗi matsayar gwamnonin jihohi game da sabon mafi ƙarancin albashi

Gwamna Uba Sani.
Kaduna za ta sauya wa makarantu sama da 300 wuri saboda matsalar tsaro Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Facebook

Shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Kaduna, Sani Kila, wanda ya wakilci Gwamna Uba Sani ya ce za a hade makarantun da ke yankunan da babu tsaro da wadanda ke wurare masu aminci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa gwamnatin Kaduna ta ɗauki matakin?

Ya ce wannan na ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka domin tsare makarantu da ƙananan yara ɗalibai daga sharri da harin ƴan bindiga.

A cewarsa, rundunar tsaron makarantu da aka kaddamar karkashin shirin gwamnatin tarayya za ta maida hankali ne wajen kare makarantu, ɗalibai da malamai daga harin ƴan ta'adda.

Kila ya kuma bayyana cewa jihar Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da ayyukan ƴan bindiga, ta'addanci, garkuwa da mutane da wasu miyagun laifuka.

Shugaban ma'aikatan ya koka kan yadda ƴan ta'adda suka lalata zamantakewa da walwalar mutane, kana suka zama barazana ga harkokin neman ilimi, The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki makarantar sakandire a Arewa, sun tafka ɓarna

An samu raguwar shiga makaranta a Kaduna

"An samu raguwar masu shiga makarantu a Kaduna, adadin waɗanda suka yi rijista a zangon karatu na 2022/2023 ya yi ƙasa da ɗalibai 200,000 idan aka kwatanta da zangon baya.
“A kananan hukumomi da dama kamar Chikun, Birnin Gwari, Kajuru, Giwa, da kuma Igabi, rashin tsaro ya tilasta rufe makarantu, lamarin da ya kara yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
"Domin tabbatar da yaran mu sun ci gaba da karatu, mun fara ƙoƙarin tashin makarantu 359 domin haɗe su da waɗanda suke a wurare masu tsaro da aminci."

- Sani Kila.

Sojoji sun samu galaba a Kaduna

A wani rahoton kuma, an ji dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan ƴan ta'adɗa masu tayar da ƙayar baya a jihohin Borno da Kaduna bayan sun yi artabu.

A jihar Borno dakarun sojojin sun hallaka wani ɗan ta'adda tare da ceto wani yaro da ƴan ta'adda suka sace a ƙaramar hukunar Nganzai ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel