Yan Bindiga Sun Sace Mata da Miji da Yaransu a Kaduna

Yan Bindiga Sun Sace Mata da Miji da Yaransu a Kaduna

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun tafka sabuwar ta'asa a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna
  • Ƴan bindigan dai sun yi awon gaba da wasu mata da miji da yaransu a ƙauyen Kinini na gundumar Kakangi da ke ƙaramar hukumar
  • Shugaban ƙungiyar cigaban masarautar Birnin Gwari (BEPU) wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya koka kan yawaitar garkuwa da mutane a yankin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutum huɗu ƴan gida ɗaya a ƙauyen Hayin Kinini a gundumar Kakangi da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

An bayyana cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Talata, inda ƴan bindigar suka kai farmaki wani gida da ke wajen ƙauyen, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

An Kama Shugaban Ƙaramar hukuma da wani bisa hannu a yunkurin kashe kakakin majalisa a Arewa

Yan bindiga sun sace mutum hudu a Kaduna
Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum hudu a Kaduna Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Shugaban ƙungiyar cigaban masarautar Birnin Gwari (BEPU), Ishaq Kasai, ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya bayyana a matsayin abin takaici.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

A kalamansa:

"Sun yi garkuwa da mai gidan, matarsa, da ƴaƴansu biyu a cikin daren ba tare da sanin mazauna ƙauyen ba. Mahaifiyar mutumin ce ta je gidansa ta gano abin da ya faru. Iyalan suna zaune a bayan garin ƙauyen."

Shugaban na BEPU ya koka da yadda ake samun yawaitar sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa a wasu ƙauyukan ƙaramar hukumar tare da rokon gwamnati ta sa baki.

Jaridar New Telegraph ta rahoto cewa a kwanakin baya ƴan bindiga sun sace wasu sababbin ma'aurata da wani limami a jihar Kaduna.

Sai dai, babu wani martani a hukumance daga rundunar ƴan sandan jihar Kaduna. Ba a samu kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ta wayar tarho ba, kuma har yanzu bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun afkawa kauyuka 10 a karamar hukuma a Kaduna

Ƴan Bindiga Sun Halaka Shugaban Makarantar Sakandare a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun tafka sabuwar ta'asa a jihar Kaduna, inda suka halaka wani shugaban makarantar sakandare.

Ƴan bindigar sun kashe shugaban makarantar sakandaren (GSS) Kuriga da ke a ƙaramar hukumar Chukun, Malam Idris Abu Sufyan, lokacin da suka yi kokarin sace shi amma ya ƙi yarda su tafi da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel