Falasdin: Amurka ta Dakatar da Taimakawa Babbar Kawarta Isra'ila da Bama Bamai

Falasdin: Amurka ta Dakatar da Taimakawa Babbar Kawarta Isra'ila da Bama Bamai

  • Kasar Amurka a karon farko ta yi jan kafa wajen taimakawa babbar kawarta, Isra’ila a harin da take kai wa kan Falasdinawa
  • Wani jami’in Amurka ya bayyana cewa an dakatar da kai wasu manyan bama-bamai Isra’ila don fargabar kai hare-hare Rafah
  • Kimanin mutane miliyan daya ne su ka nemi mafaka a yankin Rafah bayan harin sojojin Isra’ila ya tarwatsasu daga gidajensu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

USA- Biyo bayan kin bin umarni da shawarwari da kasar Isra’ila ta yi na ci gaba da kai hare-hare zirin Gaza, yanzu haka babbar kawarta Amurka, ta dakatar da sayar mata bama-bamai.

Kara karanta wannan

'Akwai manyan da ke yi wa gwamnatina makarkashiya', Gwamnan APC ya koka

Wannan shi ne karon farko da shugaban kasar Amurka, Joe Biden da ya rantse ba zai daina taimakawa Isra’ila wajen kaiwa Falasdinawa hari ba ya dan yi jan kafa.

Yakin Isra'ila kan Gaza
Amurka ta dakatar da kai bama-bamai Isra'ila Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kisan Falasdinawa ya hana Amurka kai bam

Channels Television ta tattaro cewa wani jami’i a gwamnatin Amurka ya ce an dauki matakin ne saboda fargabar Isra’ilan za ta kaiwa Falasdinawan da suka yi gudun hijira zuwa yankin Rafah hari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakin na zuwa ne bayan rahotanni sun ce rundunar sojin Isra’ila ta kwace iko da mashigar Rafah ta bangaren Gaza.

Dalilin Amurka na dakatar da taimakawa Israila

Wani babban jami’i a gwamnatin Amurka da Joe Biden ke jagoranta, ya ce sun dakatar da kai bama-bamai Isra’ila ne saboda fargabar za a yi amfani da shi kan farar hula a Rafah.

Jami'in ya bayyana cewa tun a makon da ya gabata ne Amurka ta dakatar da kai wasu manyan bama-bamai kamar yadda aka tsara za a kai tun da fari.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta dawo da lantarki a garuruwan da aka yi shekaru babu wuta a Sokoto

A rahoton da DW ta wallafa, sama da Falasdinawa Miliyan daya ne ke neman mafaka a yankin Rafah tun bayan da Isra’ila ta fara kai hare-hare Gaza a bara.

Jami’in ya ce suna ta tattaunawa kan yadda za a bullowa lamarin bama-baman.

Turkiyya ta yanke alaka da Isra’ila

A baya kun ji cewa shugaban kasar Turkiyya, Recep Erdogan ya datse alakar kasuwanci tsakanin kasarsa da Isra’ila biyo bayan hare-haren da take ci gaba da kaiwa kan fararen hula a Gaza.

Alakar da Turkutta ta dakatar ya shafi dukkanin bangarorin cinikayya kamar yadda ma’aikatar kasuwancin kasar ta bayyana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel