Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

Najeriya na daga cikin kasashe mafiya arziki a Najeriya, kuma ta na da kimanin mutanen da ya kai miliyan 200. Akwai jihohi 36 da kuma birnin tarayya guda daya. Anan an kawo goma daga ciki mafiya arziki a kasar

Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya
Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya. Hoto: NigerianInfo
Asali: Twitter

Shin ko ka san jihohin da suka fi arziki a Najeriya? Biyo mu domin samun amsoshin wannan tambayar.

Don gano wannan amsar tambayar 'Na jihohin da suka fi arziki a Najeriya?', Ya zama dole a yi la'akari da kididdigan abinda kasar ke samarwa a shekara wato GDP. Shine jimillar kudin dukkan ababen da kasar ke samarwa na albarkatu da ayyuka.

Ga dai jerin jihohin a kasa kamar yadda Legit.ng ta tattara.

10. Kaduna - Dala biliyan 10.33

Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya
Al'ummar Kaduna. Hoto: NigerianInfo
Asali: Twitter

Kaduna jiha ce da ke tsakiyar arewacin Najeriya. Yawan mutanen jihar ya kai miliyan 6.1. Kaduna na cikin jahohi mai yawan kabilu, a kasar da ke da mabanbantan kabilu fiye da 60. Arzikin jahar ya kai kimanin biliyan $10.33. Ɓangaren noma shine bangaren babban fannin samar da kudin.

9. Ogun - Dala biliyan 11

Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya
Hoton jihar Ogun daga sama. Hoto: NigerianInfo
Asali: Twitter

Ogun jiha ce da ke kudu maso yammacin Najeriya. Adadin yawan mutanen jihar ya kai mutane miliyan hudu. Akwai manya manya masana'antu kamar Protector and Gamble a Agbara, Coleman Cables a Arepo, Lafarage Cement a Ewekoro, Dangote Cement a Ibese. Arzikin jihar ya kai kimanin Dala biliyan 11.

8. Akwa Ibom - Dala biliyan 11

Akwa Ibom ta na kudancin kasar. Yawan mutanen jihar ya kai kimanin mutane miliyan 5.5 . Yankin ya na da cibiyar nazarin binciken zamani, Ibom E-library. Kabilun da ke jihar su ne Ibibio, Annang, Oron, Eket da Obolo. Arzikin jihar ya kai $11 biliyan.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe masallata 5, sunyi awon gaba da liman da mutum 40 yayin sallar Juma'a a Zamfara

7. Edo - Dala biliyan 11.89

Yawan mutanen Edo ya kai mutane miliyan 3.5 da arzikin da ya kai kimanin $11.89 biliyan. Edo jiha ce da ke da abubuwan bude ido, kamar mutum-mutumin Emotan a Benin City da tafkin Agenebodo. Tana cikin jihohi goma mafiya arziki a Najeriya.

6. Kano - Dala biliyan 12.39

Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya
Kano cikin hoto. Hoto: Kano
Asali: Twitter

A kiyasance, yawan mutanen Kano ya kai kimanin mutane miliyan 11 da arzikin da ya kai $12.39 biliyan. Kano jiha ce da ta shahara wajen samar da kirgi da fata. Tana kuma samar da barkono, ƙaro, tafarnuwa, auduga, waken suya da kantu.

5. Imo - Dala biliyan 14.21

Imo jiha ce da ke kudu maso gabashin Najeriya. Arzikin jihar ya kai kimanin biliyan $14.21. Imo ta na da yalwar ma'adanai, kamar zinc, iskar gas, danyen man fetur, farar kasa, da kuma yashi. Akwai rijiyoyin man fetur fiye da 163 a Imo. Manyan kamfanunuwan man fetur a jihar sune Agip, Royal Dutch Shell, Chevron Corporation da Addax Petroleum.

4. Oyo - Dala biliyan 16.12

Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya
Taswirar Jihar Oyo. Hoto: Oyolove
Asali: Twitter

Oyo ta na kudu maso yamma a Najeriya. Tana cikin jihohi 20 mafiya arziki. Yawan mutanen Oyo ya kai dala biliyan 16.12. Bangaren noma ne babban hanyar samar da kudi. Oyo tana samar da kashu, kwakar manja, kwakwa, agada, shinkafa, gero, rogo, doya da masara.

KU KARANTA: An kama ƴan fashi da suka ƙware wurin kashe masu babur a Katsina

3. Delta - Dala biliyan 16.75

Delta jiha ce a kudancin Najeriya. Yawan mutanen jihar sun kai miliyan 4.1. Arzikin jihar ya kai biliyan $16.75. Akwai arzikin ma'adanai, kamar farar kasa, duwatsun kwalliya, kasar kwalta, kaolin da kuma tabo. Delta tana cikin jihohi masu arzikin ɗanyen mai da iskar gas a Najeriya.

2. Rivers - Dala biliyan 21.17

Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya
Taswirar JIhar Rivers. Hoto: Rivers
Asali: Twitter

Wannan jihar tana cikin jihohi mafi yalwar arziki a Najeriya. Ta na da girman kilo mita 11,077. Yawan mutanen jihar ya kai kimanin mutane miliyan 5.2. Kuma arzikin jihar ya kai dala biliyan 21.17. Akwai yalwar iskar gas da danyen mai. Fiye da kaso 60 na danyen man Najeriya daga can yake fitowa. Kuma anan tashar jiragen ruwa ta ke.

1. Lagos - Dala biliyan 33.68

Lagos ce ta daya a jerin, kuma ita ce jiha mafi ci gaba a Najeriya.

Tana yankin kudu maso yamma, tana da girman kilo mita 3,577 kuma arzikin jihar ya kai kimanin biliyan $33.68. Lagos ita ce jiha mafi muhimmanci ga tattalin arzikin kasar, akwai birnin Lagos, birni mafi fadi a Najeriya. Babbar cibiyar kasuwanci ce kuma zata zama ta biyar a arziki a Afirika, da a ce kasa ce.

A wani labarin, Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya siffanta Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin 'raɓa' a yayin da ya ke tsokaci a kan wani littafi da aka rubuta kan shugaban kasar mai taken "The Buhari in Us".

Yahaya Bello ya furta hakan ne cikin wani faifan bidiyo da ya bazu a shafunkan sada zumunta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164