Badakalar N2.7bn: Ministan Buhari, Hadi Sirika da Diyarsa Sun Isa Kotu a Abuja

Badakalar N2.7bn: Ministan Buhari, Hadi Sirika da Diyarsa Sun Isa Kotu a Abuja

  • A shirye-shiryen fara fuskantar shari'a, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da ɗiyarsa Fatima sun isa babbar kotun tarayya
  • Hukumar EFCC ta shirya gurfanar da tsohon ministan a gaban mai shari'a kan yadda aka yi da wasu kuɗin kwangila N2.7bn
  • Sirika, ɗan asalin jihar Katsina ya yi aiki ne a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari kuma yana cikin waɗanda EFCC ta taso a gaba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da ɗiyarsa, Fatima Hadi Sirika, sun isa harabar babbar kotun tarayya mai zama a birnin Abuja.

Tsohon ministan da ɗiyarsa sun dira kotun ne domin mutunta shirin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) na gurfanar da su a gaban ƙuliya.

Kara karanta wannan

Tsohon minista Hadi Sirika ya kafa misali da annabawa yayin da ya gurfana a gaban kotu

Tsohon ministan Buhari, Hadi Sirika.
Hadi Sirika da ɗiyarsa sun isa babbar kotun tarayya mai zama a Abuja Hoto: Hadi Sirika
Asali: Facebook

Hadi Sirika ya isa kotu domin shari'a

EFCC za ta gurfanar da Hadi Sirika ne kan tuhume-tuhumen sama da faɗi da kuɗin talakawa da kuma cin amanar ofis, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa tsohon ministan ya isa harabar babbar kotun tarayya da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar yau Alhamis, 9 ga watan Mayu, 2024.

Hukumar EFCC na tuhumarsu da aikata laifuffuka 6 da suka shafi badaƙalar kwangiloli na N2.7bn.

Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka an fara karanto masu tuhume-tuhumen da ake masu a gaban alƙali.

A rahoton Daily Trust, mutumin da ake tuhuma na uku wanda aka gurfanar da shi tare da Sirika da diyarsa shi ne surukinsa, Jalal Sule Hamma.

Kamfanin Al-Duraq Investment Limited na cikin waɗanda ake tuhuma a ƙarar. Dukkansu sun musanta aikata laifukan da ake tuhumar su da su.

Kara karanta wannan

Plateau: Ƴan bindiga sun kashe bayin Allah, sun tafka mummunar ɓarna a Arewa

EFCC ta roki a hanzarta shari'ar

Lauyan hukumar EFCC, Rotimi Jacobs, ya roƙi kotun ta gaggauta sauraron karar har zuwa ƙarshe.

Mista Jacobs ya ce hukumar ta bayar da belin wadanda ake tuhumar da sharaɗin za su sake kawo kansu ranar 19 ga watan Afrilu, amma ba su dawo ba.

Ya kara da cewa tunda sun bayyana gaban kotu ya kamata a tabbatar da suna zuwa kowane zama domin kada a samu jinkiri a shari’ar babu gaira babu dalili.

Majalisa za ta binciki kwangilar titin Kalaba

A wani rahoton kuma majalisar wakilai ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike kan yadda aka bayar da kwangilar babbar hanyar Legas zuwa Calabar.

Hon. Austin Achado (APC, Benue) ne ya gabatar da kudirin gaggawa kan aikin ginin a yayin majalisar na yau Alhamis, 9 ga Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel