Yan Ta'adda Sun Nemi Makudan Kudin Fansa Kan Mutum 31 da Suka Sace a Arewa, Sun Tura da Sako

Yan Ta'adda Sun Nemi Makudan Kudin Fansa Kan Mutum 31 da Suka Sace a Arewa, Sun Tura da Sako

  • Miyagun ƴan ta'addan da suka sace mutum 31 a ƙaramar Batsari ta jihar Katsina sun aike da saƙon kan kuɗin fansan da za a ba su
  • Ƴan bindigan sun buƙaci mutanen ƙauyen da suka tafka wannan ta'asa da su haɗa musu N60m
  • Mazauna ƙauyen dai sun koka cewa ba za su iya haɗa waɗannan kuɗaɗen ba inda suka buƙaci gwamnati ta kawo musu agaji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Ƴan ta’addan da suka yi garkuwa da mutane 31 a Tashar Nagulle da ke ƙaramar Hukumar Batsari ta jihar Katsina sun faɗi kuɗin fansan da za a ba su.

Jaridar Premium Times ta kawo rahoto cewa mazauna yankin sun ce ƴan ta'addan suna neman a biya su kuɗin fansa Naira miliyan 60 domin su sake su.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun badda kama sun halaka jami'an yan sanda a Arewa

Yan bindiga sun nemi kudin fansa a Katsina
Yan ta'adda sun bukaci a ba su kudin fansa N60m a Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Twitter

An sace mutanen ne a wani harin dare da aka kai ƙauyen a ranar Lahadin da ta gabata, lokacin da ƴan ta’addan sanye da kayan sojoji suka yaudari mazauna yankin cewa sojoji ne da aka tura domin su kare su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan ta’addan sun yi amfani da ɗaya daga cikin wayoyin mutanen da suka sace wajen kiran ƴan uwansa tare da ba da umarnin a kai wayar ga shugaban gundumar.

Wani majiya da aka yi tattaunawar a gabansa ya bayyana cewa:

"Mu talakawa ne, ba ma iya samar da Naira 60,000 ba ballantana a ce miliyoyin Naira.
"Don haka babu ma’ana a yi maganar samun Naira miliyan 60 daga gare mu. Muna kira ga hukumomi da su kawo mana agaji domin komai ya taɓarɓare.
"Ba za mu iya zuwa gonakinmu ba, haka ma ba mu da hanyar da za mu yi amfani da kasuwannin cikin gida, don haka ta yaya zamu iya tara N60m."

Kara karanta wannan

Babbar nasara: An kashe manyan ƴan bindiga 3 yayin musayar wuta a dajin iyakar Abuja da Kaduna

Wani shugaban addini a yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ƴan ta’addan sun fusata a lokacin da mazauna yankin suka ce ba za su iya tara Naira miliyan 60 ba.

Ƴan Sanda Sun Halaka Ɗan Bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta samu nasarar daƙile wani harin ƴan bindiga a jihar.

Ƴan sandan sun kuma halaka ɗan bindiga ɗaya a yayin daƙile yunƙurin garkuwa da mutanen da ƴan bindigan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel