Babbar Nasara: An Kashe Manyan Ƴan Bindiga 3 Yayin Musayar Wuta a Dajin Iyakar Abuja da Kaduna

Babbar Nasara: An Kashe Manyan Ƴan Bindiga 3 Yayin Musayar Wuta a Dajin Iyakar Abuja da Kaduna

  • Ƴan sanda sun halaka ƙasurgumin ɗan bindiga mai garkuwa da mutane da wasu hatsabibai guda biyu a birnin Abuja
  • Kaƙakin rundunar ƴan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da haka a Abuja ranar Jumu'a, 26 ga watan Janairu, 2024
  • Yan ta'addan sun baƙuncin lahira ne a hannun dakaru na musamman na IGP da jami'an rundunar ƴan sandan FCT a wani dajin Bwari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Dakarun ƴan sanda na tawaga ta musamman da jami'an rundunar ƴan sandan Abuja sun yi nasarar halaka manyan ƴan bindiga 3 a dajin da ke Bwari, Abuja.

The Nation ta ce ƴan sandan sun sheƙe ƴan bindigar ne da sanyin safiyar yau Jumu'a, 26 ga watan Janairu, 2024 da misalin karfe 2:00 na dare a wani daji da ya haɗa Abuja da Kaduna.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da yawa sun baƙunci lahira yayin da suka kai hari a jihar arewa, mutum 2 sun tsira

Sufetan ƴan sanda na ƙasa, IGP Kayode.
Yan sanda sun halaka kasurgumin mai garkuwa da wasu biyu a Abuja Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Daga cikin ƴan bindigan da suka sheƙa barzahu harda wani hatsabibin mai garkuwa da mutane kuma shugaban tawaga, Mai Gemu, wanda aka fi sani da Godara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Godara tare da ƴan tawagarsa sun jima suna kai hare-haren kan mazauna babban birnin tarayya da maƙotan jihohi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sanda ta ƙasa, Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Juma’a yayin nuna mutum 20 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.

Yan sanda sun yi artabu da ƴan bindiga

Adejobi ya ce jami'an tsaron sun yi artabu da tawagar ƴan bindigar a dajin, inda suka kashe uku daga cikinsu kuma Magamu, shugaban ƴan bindigar na cikin waɗanda aka kashe.

A rahoton Daily Trust, kakakin ƴan sandan ya ce:

"Da sanyin safiyar yau Juma’a, jami’an DFI-IRT suka yi artabu da wasu ‘yan bindiga a yankin, inda suka kashe 3 daga cikinsu ciki har da shugaban tawagar mai suna Mai Gemu Godara.

Kara karanta wannan

Filato: Asirin wasu mutane da ake zargi da hannu a kashe bayin Allah sama da 100 ya tonu a Arewa

"Zamu iya faɗa da izza cewa an tarwatsa sansanin waɗannan ƴan ta'adda, daga yau duk wata tawagar masu garkuwa a Bwari da iyakokin Kaduna sun yi sallama da zaman lafiya domin ba zamu barsu ba."

Masu garkuwa sun nemi fansa N200m

A wani rahoton kuma Ƴan bindigan da suka yi garkuwa da shugaban PDP na jihar Legas da wasu jiga-jigai sun nemi N200m a matsayin kuɗin fansa.

Mista Philip Aivoji da wasu mambobin PDP na hanyar dawowa daga Ibadan ranar Alhamis lokacin da ƴan bindiga suka sace su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel