"Yadda Ake Zuwa Najeriya Daga Turai da Indiya Domin Neman Lafiya", Ministan Tinubu

"Yadda Ake Zuwa Najeriya Daga Turai da Indiya Domin Neman Lafiya", Ministan Tinubu

  • Tunji Alausa, karamin Ministan lafiya a Najeriya ya sha alwashin ci gaba da inganta bangaren lafiya a kasar zuwa karkara
  • Dakta Alausa ya bayyana irin ci gaba da aka samu a Najeriya a bangaren kiwon lafiya da ke jawo hankalin kasashen duniya
  • Ministan ya ce mutane daga Nahiyar Turai da Indiya da kasashen Afrika suna zuwa har cikin Najeriya domin neman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Karamin Ministan lafiya, Tunji Alausa ya bayyana yadda suka inganta bangaren lafiya a Najeriya.

Tunji Alausa ya ce mutane daga Nahiyar Turai da Indiya da sauran ƙasashen Afirka suna zuwa Najeriya neman lafiya.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata ku sani game da tafiyar Tinubu da aka ce ya 'ɓata' kafin ya dawo

Ministan Tinubu ya fadi yadda mutane daga indiya da Turai ke zuwa neman lafiya
Ministan lafiya, Tunji Alausa ya fadi yadda Bola Tinubu ke inganta bangaren lafiya. Hoto: @officialABAT, @DrTunjiAlausa.
Asali: Twitter

Musabbabin zuwa Najeriya neman lafiya

Ministan ya bayyana wannan cigaba ne a yayin wata hira da Arise TV a ranar Talata 7 ga watan Mayu a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alausa ya ce musabbabin tururuwa zuwa Najeriya shi ne harkokin lafiya da sauki a kasar ba kamar sauran ƙasashe ba.

"Ka je asibiti a Legas, za ka ga mutane daga Nahiyar Turai da Indiya da sauran ƙasashen Afrika suna zuwa domin neman lafiya a Najeriya."
"Samun kayayyakin tiyata ya na da sauki a Najeriya, a yanzu muna da asibitoci da ke sauya halitta kusan 900 a fadin Najeriya."
"Mutane suna zuwa domin yi musu tiyata da za ta sauya surarsu, a Legas akwai cibiyoyin ciwon daji wadanda ke da inganci fiye da kasashe da dama a duniya."

- Tunji Alausa

Alausa ya fadi kokarin Tinubu kan lafiya

Kara karanta wannan

Tinubu yana kasar waje saboda rashin lafiya? Minista ya fadi gaskiya

Karamin Ministan ya ce suna kara inganta harkokin lafiya ba iya Legas kadai ba har sauran sassan Najeriya baki daya.

Alausa ya ce a yanzu sun himmatu wurin inganta harkokin lafiya zuwa karkara domin samar da sauki ga al'umma.

Ya ce Tinubu ya umarce su da su fadada inshora ta lafiya daga mutane miliyan bakwai zuwa aƙalla miliyan 50 a Najeriya.

Jigon APC ya magantu kan matsalar El-Rufai

A wani labarin, jigon APC a Najeriya, Jesutega Onakpasa ya zargi wasu 'yan siyasa da jefa Nasir El-Rufai da Yahaya Bello a halin da suke ciki.

Onakpasa ya ce abin takaici ne yadda tsofaffin gwamnonin suka bayar da gudunmawa ga jami'yyar amma an yi watsi dasu a yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel