Yan Sanda Sun Kashe Masu Garkuwa da Mutane, An Kwato Miliyoyin Kudin Fansa

Yan Sanda Sun Kashe Masu Garkuwa da Mutane, An Kwato Miliyoyin Kudin Fansa

  • Rundunar ƴan sanda a jihar Ogun ta tabbatar da nasarar kashen masu garkuwa da mutane a kan hanyar Sagamu tare da kwato kudaden fansa
  • Kakakin rundunar'yan sandan jihar ne, SP Omolola Odutola ta bayyana haka ga manema labarai a jiya Talata, 7 ga watan Mayu
  • SP Odutola ta fadi yadda suka yi da gawar wadanda aka kashe din tare da bayyana matakan da suka dauka kan sauran da suka gudu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta sanar da kashe wasu masu garkuwa da mutane guda biyu a jiya Talata.

Nigerian Police
Yan sanda sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a jihar Ogun. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane

Kara karanta wannan

Miyagu sun tafka ɓarna, sun yi garkuwa da fasinjojin jirgin ruwa a Najeriya

Masu garkuwa da mutanen ne ake zargi da fitinar matafiya a kan hanyar Sagamu da ta hada da hanyar Ijebu-Ode-Benin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton jaridar Punch ya tabbatar da cewa rundunar 'yan sanda ta fafata da masu garkuwar kafin daga bisani su yi nasara a kansu.

Biyo bayan samun bayanan sirri da haɗaka da 'yan banga, rundunar ta kai farmaki ga bata garin da misalin karfe 4:00 na safiyar Talata.

Nasarar da 'yan sanda suka samu

Artabun da aka yi ya jawo ceto wasu mutane 'yan asalin ƙasar Hindu guda uku wadanda aka yi garkuwa dasu ranar 3 ga watan Mayu.

Sun kuma sanar da kwato kudaden fansa da masu garkuwar suka tara wadda suka kai Naira miliyan 7.9 da kudin Indiya rupee 1500, cewar Tribune Online.

Har ila yau 'yan sanda sun kwato bindiga kirar AK47 guda biyu, bindigar gida guda daya, takobi guda daya da wayar hannu guda daya da kuma harsashi guda 65.

Kara karanta wannan

An gurfanar da mutumin da ake zargi da safarar makamai ga 'yan bindiga a Kano

Jawabin 'yan sandan jihar Ogun

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin a bayanai da ta turawa manema labarai.

A cewar kakakin, manajan kamfanin Breeze Nigeria Limited ya yi musu kiran gaggawa a kan 'yan bindiga sun kai hari kan tawagar ma'aikatansa.

Biyo bayan kiran ne sai rundunar yaki da garkuwa da mutane ta bazama neman yan bindigar tare da hadin gwiwar 'yan banga.

Kakakin ta tabbatar da cewa a halin yanzu gawar wadanda aka kashe din tana dakin ajiyar hawa yayin da ake bincike kan kamo waɗanda suka gudun.

Yan bindiga sun kai hari Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa akalla mutane shida ne suka mutu yayin da wasu takwas suka samu raunuka a wani hari da 'yan bindiga suka kai a jihar Kaduna.

Daniel Amos, 'dan majalisa mai wakiltar mazabar Jema’a/Sanga a majalisar wakilai, ya ce an kai harin ne a kauyen Ambe da ke Sanga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng