Amarya Ta Yaudari Kawayenta Su 60 Bayan Ta Siyar Masu da Ankon Biki N60k, Ta Tsere Kasar Waje

Amarya Ta Yaudari Kawayenta Su 60 Bayan Ta Siyar Masu da Ankon Biki N60k, Ta Tsere Kasar Waje

  • Bayan ta fake da sunan 'aure', wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta shammaci kawayenta su 60
  • Labarin ya nuna cewa ta siyarwa kawayen nata ankon bikinta da mafici kan N60k kowannensu gabannin bikinta
  • Yayin da suka isa wajen da ta fada masu a matsayin inda za a yi shagalin, sai suka gane cewa yaudararsu tayi ta hanyar tserewa da kudinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata mai amfani da dandalin X, @AkiMarlin, ta ba da labarin yadda wata yar kasuwa, wacce ke sana'arta a kusa da jami'ar jihar Imo, Owerri, ta yaudari kawayenta kimanin su 60.

A wani labari da ya yi fice a dandalin X, @AkiMarlin ta ce yar kasuwar ta sayarwa kawayen nata su 60 ankon biki da mafici gabannin bikinta.

Kara karanta wannan

“Wannan ramar ba ta maki kyau ba” Sabon hoton Hadiza Gabon ya haddasa cece-kuce

Matashiya ta tsere bayan siyarwa kawayenta da ankon bikin karya
An yi amfani da hoton don misali ne kawai Hoto: Djelics, Aaron Foster
Asali: Getty Images

Amarya ta lale kudin kawayenta

Ta saida masu da ankon bikin kan N50k sannan mafici kan N10k. @AkiMarlin ta kara da cewar ta fada masu wajen da za a yi shagalin wankan amarya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lokacin da kawayen wadanda basu yi zargin komai ba suka isa wajen biki, sai suka neme ta suka rasa.

Washegarin ranar, sai suka gano cewa ta yi kaura zuwa kasar Canada sannan kuma babu auren da za ta yi a gaske. @AkiMarlin ta rubuta:

"Wato wannan budurwar ta siyarwa kimanin kawayenta 60 anko kan N50k da mafici kan 10k.
"Ta fadi wajen da za a yi wankan amarya a wani otal.
"Wasu daga cikin kawayenta sun isa wajen sannan bata kasance a wajen ba.
"A takaicen takaitawa ta tsere Zuwa Canada washegarin ranar, magana ta gaskiya babu wani aure.

Kara karanta wannan

Mai ciki ta haihu a tsaye yayin da ake cigaba da kashe Bayin Allah a Filato

"Shahararriyar kasuwa ce a kusa da IMSU."

Kalli wallafar a kasa:

Jama'a sun yi martani

@OloriebiINvogue ta ce:

"Bata ba su kayan ba sannan ta fada masu wajen wankan amaryar? Wani kaya za su sa su je bikin?"

@Irunnia_ ta ce:

"Kowa na maganar damfarar amma ni ina nan ina mamakin yadda ta samu kawaye 60.
"Bana iya zama da 10."

@FunmiKolz ta ce:

"Kenan babu hotunan ma'auratan ko wani abu? Kawai suka damka mata 60k haka kawai?"

@UncleMohamz ta ce:

"Kenan bata ajiye masu hotunan auren ba? ko katin gayyata? Sannan suka aika mata kudin haka kawai?"

Budurwa ta yi murnar tsarkake kanta

A wani labarin kuma, wata yar TikTok, @ntombi_nkosi, ta yi murnar tsarkake kanta tare da kauracewa mu'amalar kwanciya da 'da namiji.

Tana cikin shekaru biyar kenan rabonta da yin mu'amalar kwanciya da 'da namiji, kan haka ne ta saki bidiyo tana mai farin ciki da taka rawa yayin da take sanar da duniya wannan ci gaban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel