“Tsohuwar Dalibata Yanzu Amaryar Mijina”: Matar Aure Ta Magantu Yayin da Mijinta Ya Kara Aure

“Tsohuwar Dalibata Yanzu Amaryar Mijina”: Matar Aure Ta Magantu Yayin da Mijinta Ya Kara Aure

  • Bayan mijinta na shekaru 20 ya kara aure, wata yar kasuwa ta yi martani kan ci gaban a dandalin Facebook
  • A cewarta, ta samu labarin auren da mijinta ke shirin karawa mako guda kafin bikin sannan ta jinjinawa mijinta kan yadda bai yi mata boye-boye ba
  • Da take maraba da amaryar, ta aika sako mai tsuma zuciya ga tsohuwar dalibarta da ta zama kishiyarta

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata yar Najeriya mai suna, Fatima Yusuf Nuhu, ta aika kalamai masu dadi ga mijinta yayin da ya auri tsohuwar dalibarta a matsayin mata ta biyu.

A ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, matar ta saki katin gayyatar auren mijinta, tana mai gayyatar mutane da su zo daurin auren a ranar 2 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

"Zai shafe watanni 4:" Kotu ta tura wani matashi magarkama saboda satar doya a Abuja

Matar aure ta marawa mijinta baya don ya kara aure
“Tsohuwar Dalibata Yanzu Amaryar Mijina”: Matar Aure Ta Magantu Yayin da Mijinta Ya Kara Aure Hoto: Fatima Yusuf Nuhu
Asali: Facebook

A wani rubutun da ta yi a Facebook a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba, yar kasuwar ta magantu cewa ta san batun auren ne mako guda kafin ayi shi sannan ta yaba ma mijinta kan kin boye mata komai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar ta bayyana cewa sun shafe tsawon shekaru 20 da aure sannan ta jaddada goyon bayanta ga matakin da mijinta ya dauka na yin amarya.

Fatima ta karfafawa mata gwiwar barin mazajensu su kara aure

Ta kare abun da mijinta ya yi a matsayin hanyar rage yawan mata marasa aure a gari da kuma kira ga mata da su marawa mazajensu baya idan suka yanke shawarar kara aure. Ta ce:

"....Duba ga yawan mata marasa aure a yau da sauye-sauyen al'umma da muke fuskanta, na ga ya dace in bude gidanmu da zuciyar mijina ga wata mace.

Kara karanta wannan

Amarya ta fasa aurenta yayin da angon ya gindaya mata sharudda 4 gabannin aurensu

"Ta wannan sakon, ina nufin kira da karfafawa mata gwiwar marawa mazajensu da suka zabi auren mace fiye da daya baya."

Fatima na da sako zuwa ga amaryar

Da take ci gaba da rubutu, tace diyarta za ta rungumi kowani mataki a aure sanin cewa ita ma ta yi hakan.

Ta yi wa amaryar maraba da zuwa da kalamai masu dadi. Ta rubuta:

"Daga yanzu, diyata a shirye take ta rungumi kowace irin matsayi- imma mace ta farko, ta biyu, ta uku, ko ta hudu - sanin mahaifiyarta tana mutuntawa kuma ta yarda da shawarar mahaifinta na kara mata.

"Ina taya amarya murna, kuma ina fatan rayuwa mai aminci tare da mijinmu."

Mutane sun jinjinawa Fatima Yusuf Nuhu

Aisha Abubakr Sulayman ta ce:

"Mashaa Allah Quwata ya yar'uwa, na jinjinawa karfinki wajen marawa mijinki baya Allah ya albarkace ki sannan ya yi maki jagora wajen gina gida mai cike da farin ciki❤️."

Kara karanta wannan

Yadda yaran turawa da mahaifinsu suka sharbi kuka a filin jirgi kan rabuwa da mai aikinsu

Mahmoud Sallawu ya ce:

"Na taya ki murna gimbiyata. Gida mai cike da zaman lafiya nake yi maki addu'a. Na ji sha;awar karfin gwiwarki da marawa mijinki baya da kika yi. Na tayaki murna."

Habiba Lami Mohammed ta ce:

"Ma shaa Allah da farko na jinjinawa karfin gwiwarki, lallai ke daya ce tamkar da dubu! Abun da kika yi da karfin gwiwarki na bukatar ayi koyi da ke. Allah ya jagoranci nutsuwar zuciyarki Ameen. Na tayaki murna yar'uwa."

Idris Kolo ya ce:

"Wallahi kina daya daga cikin matan Al-jannah da fiyayyen halitta ya bayyana. Lallai ke madubin dubawa ce da kika cancanci ayi koyi da ke. Allah ya baki nutsuwar zuciya sannan ya fisshe ki kaidin shaidan."

Amarya ta fasa aure gabannin biki

A wani labarin, mun ji cewa wata yar Najeriya ta nuna damuwa kan bukatu masu ban mamaki da angonta ya nema wata daya kafin bikinsu.

A wasu jerin hira da @dexterouz11 ya wallafa a Twitter, mai shirin zama amaryar ta bayyana cewa yana so ta shiga kungiyar asiri sannan ta yi rantsuwar zama mai gaskiya, tare da zubar jini da mutuwa idan ta ci amanarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel