“Wannan Ramar Bata Maki Kyau Ba” Sabon Hoton Hadiza Gabon Ya Haddasa Cece-Kuce

“Wannan Ramar Bata Maki Kyau Ba” Sabon Hoton Hadiza Gabon Ya Haddasa Cece-Kuce

  • Shahararriyar jarumar Kannywood Hadiza Gabon ta saki sabon hotonta a dandalinta na soshiyal midiya kuma ya haddasa cece-kuce
  • Yayin da wasu ke yaba kyan jarumar, wasu na ganin sam rama bata yi mata kyau ba cewa ta fi a yar duma-daumar ta
  • Sai dai ga dukkan alamu jarumar ta saka hoton don ayi magana ne domin ta yi shagube ga masu yin kwamet a kasan hoton

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum.

Fitacciyar jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon Aliyu Gabon, ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta saki wani sabon hotonta.

A baya dai jarumar ta kasance irin dirarrun matan nan wadanda ake kira da yan duma-duma.

Hadiza Gabon lokacin da take da kiba da yanzu
“Wannan Ramar Bemaki Kyau Ba” Sabon Hoton Hadiza Gabon Ya Haddasa Cece-kuce Hoto: adizatou
Asali: Instagram

Sai dai kuma a yan baya-bayan nan ana ta ganin sauyi tattare da jarumar wadanda alamu suka nuna tana kokarin rage nauyi da kitse a jikinta.

Kara karanta wannan

Amarya ta yaudari kawayenta su 60 bayan ta siyar masu da ankon biki N60k, ta tsere kasar waje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin da ya haddasa cece-kuce musamman a tsakanin masoya da mabiya shafukanta na soshiyal midiya.

Yayin da wasu ke ganin yar ramar da tayi ta yi mata kyau, wasu sun ce sam ta fi kyan gani a lokacin da take yar duma-dumanta.

Cece-kucen ya kara kamari ne bayan Hadiza ta saki wani sabon hotonta a shafinta na Instagram tare da yin shagube ga masu tofa albarkacin bakunanta kan yadda take burin ganin kanta.

Ta rubuta a kasan hoton cewa:

"Toh yan kwament sannunku in ki samry "

Jama'a sun yi martani kan sabon hoton Hadiza Gabon

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:

isahahmadrufai ya yi martani:

"Indai haka sliming yake maida mutum yakoma kalar tausayi kamar Wanda yatashi daga jiya to babuni Babu sliming har abada "

sarah_hussain_eyser ta ce:

Kara karanta wannan

Tinubu zai mayar da babban birnin tarayyar Najeriya Legas? Sanata Shehu Sani

"Kayi kiba Ance Kayi kiba kai slimming nan ma baa Barka ba oh ni "

massarees_makeover ta ce:

"Gskia kinfi kyau da qiba dama bakiyi slimming ba"

maryamishaq19 ta yi martani:

"Wannan ramar bemaki kyau ba ita kiba Dede ay alfarmace."

muazurahama ta ce:

"Allah ka rabamu da ciwon rama amma Maganar gaskiya kinfi kyau kina yar duma dumanki hajiyata"

mustapherh__:

"Waeni su hadiza dole sae anyi yan matanci ki yarda da lokaci kawae ki cigaba da tafia hajia"

bushrah_jaafar:

"Hadizatou Wlh da kika rame bakiyi kyau ba mgn gaskiya fa "

auntyzarahcollection_company:

"Kinfi kyau ahaka Masha Allah kiba aibada dadi Kuma kutuna da hadisin manxon Allah s a w dayakecewa kufadi alkhairi kokuyi shiru"

ilyasuhassana:

"Zan fada gsky gaba da gaba Hadiza da kibarki kinfi kyau wlh wannan ramar tayi yawa haka masha Allah plz ki dan koma yadda kike dumur dumur"

fsi_collection_and_sent_:

"Gaskiya Abun kuma yayi yawa ,mu masoyan ki kına ja mana magana pls ki tsaya haka nan ramar tayi yawa."

Kara karanta wannan

Budurwa ta yi murnar shafe shekaru 5 ba tare da namiji ya kusanceta ba, mutane sun yi martani

Jaruma Hadiza Gabon ta koka

A wani labarin kuma, mun ji a baya cewa Jaruma Hadiza Aliyu Gabon, ta sanar da Kotun shari'ar Musulunci da ke Kaduna cewa rayuwarta na cikin haɗari.

Wani mutum mai suna Bala Musa ne ya kai ƙarar Jarumar ne bisa zargin ta ƙi aurensa bayan kashe mata kuɗi N396,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel