Bayan Kashe Nabeeha, ’Yan Bindiga Sun Kuma Kashe Wata Daliba, an Samu Karin Bayani

Bayan Kashe Nabeeha, ’Yan Bindiga Sun Kuma Kashe Wata Daliba, an Samu Karin Bayani

  • Yan Najeriya musamman masu amfani da shafukan sada zumunta sun nuna bacin rai kan kashe Nabeeha da Folorunsho a Abuja
  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun sace Folorunsho tare da mahaifiyarta da 'yan uwanta uku mako biyu baya
  • Yan bindigar sun jefar da gawarwakin mutane hudu, mata uku da namiji daya, wadanda aka shaida Nabeeha da Folorunsho a cikin su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun bayyana bacin ransu biyo bayan kashe wata Mis Folorunsho Ariyo tare da Nabeeha Al-Kadriyar da 'yan bindiga suka yi a Abuja.

Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan bindigar sun jefar da gawarwakin mutane hudu da suka kashe a kan hanyar Bwari zuwa Jere SCC a karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Badakalar naira miliyan 30: Kotu ta aika tsohon dan majalisar Kaduna magarkama

Yan bindiga sun sake kashe wata daliba a Abuja
Yan bindiga sun sake kashe wata daliba bayan kashe Nabeeha, an samu karin bayani. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Yadda aka yi garkuda wa iyalan Folorunsho da na Nabeeha

Daga cikin gawarwakin da aka duba, akwai wata dalibar makarantar sakandare mai suna Folorunsho Ariyo, wacce ta ke 'ya ga babban jami’in shari’a na hukumar NUC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sannan an ga gawar dalibar aji 400 a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, Nabeeha Al-Kadriyar, Leadership ta ruwaito.

Yayin da aka yi garkuwa da Ariyo tare da mahaifiyarta da ’yan uwanta uku mako biyu da suka gabata, an kama Nabeeha tare da mahaifinta da kuma ‘yan uwanta mata biyar a ranar 9 ga watan Janairu.

An mika gawar Nabeeha da Folorunsho ga 'yan uwansu

A zantawarsa da Aminiya, kawun Nabeeha ya ce sun gano gawarwakin wasu mutane uku da suka mutu – mata biyu da namiji a lokacin da suka je dauko gawar ‘yar tasu.

Kara karanta wannan

EFCC: Kotu ta fara zaman shari'ar tsohon ministan da ake tuhuma da kwamushe dala biliyan 6

Daily Trust ta tattaro cewa an aika gawar Ariyo ga iyalanta daga babban asibitin Umaru Musa Yar’adua da ke Sabon-Wuse a jihar Neja, inda ‘yan sanda suka ajiye ta.

An yi jana’izar yarinyar ne a ranar Lahadi, 14 ga watan Janairu, 2024, a makabartar Dutse, Abuja, yayin da sauran ‘yan uwansu ke a tsare a hannun wadanda suka sace su.

Mazauna garin Bagye da Pashin sun shiga rudani

Wani shugaban al’umma a yankin, John Alpha Dogo, ya ce ‘yan bindigar sun ja mutanen zuwa wurin a daren Juma’a inda suka kashe su.

Lamarin dai ya haifar da rudani a cikin garuruwan biyu na Bagye da Pashin a cikin masarautar Dnatan, inda mazauna garin suka fice cikin rudani saboda fargaba.

A halin da ake ciki, cikakken bayani game da kisan Ariyo ya haifar da fushi daga masu amfani da shafin X, tare da yin kira da a kawo karshen rashin tsaro a babban birnin kasar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace malamin jami’ar tarayya a Zamfara

Yan bindiga sun kashe Nabeeha, dalibar jami'ar ABU Zariya

A wani labarin makamancin wannan, kun ji cewa 'yan bindiga sun kashe Nabeeha, daya daga cikin mata 6, 'yan gida daya da 'yan bindiga suka sace a Abuja.

A ranar Juma'a ne aka ruwaito 'yan bindigar sun kashe Nabeeha, bayan da suka nemi kudin fansar naira miliyan 60 daga mahaifin yaran Alhaji Mansoor Al-Kadriyar amma ba su samu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel