Ministan Tinubu Na Tsaka Mai Wuya, EFCC Ta Waiwayi Binciken Da Ake Zarginsa Da Wawure N70bn

Ministan Tinubu Na Tsaka Mai Wuya, EFCC Ta Waiwayi Binciken Da Ake Zarginsa Da Wawure N70bn

  • Shugaban hukumar EFCC ya yi alƙawarin sake nazari kan binciken Matawalle bisa zargin wawure N70bn daga baitul malin Zamfara
  • Ola Olukoyede ya ce zai kakkaɓe fayil din binciken ya dawo ɗanye domin tun da ya fara aiki a EFCC yake duba kesa-kesan da ya gada
  • Ya faɗi haka ne ta bakin daraktan hulɗa da jama'a na EFCC yayin zanga-zangar wata ƙungiya a hedkwata da ke Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban hukumar yaƙi da rashawa (EFCC), Ola Olukoyede, ya sha alwashin sake tado da binciken karamin ministan tsaro, Bello Matawalle kan zargin karkatar da kudi N70bn.

Kamar yadda jaridar Punch ta tattaro, shugaban EFCC ya lashi takobin bankaɗo fayil ɗin binciken Matawalle tare da sake nazari kan kes din badaƙar kuɗin lokacin yana gwamnan Zamfara.

Kara karanta wannan

EFCC: Kotu ta fara zaman shari'ar tsohon ministan da ake tuhuma da kwamushe dala biliyan 6

EFCC zata sake buɗe kundin binciken Matawalle.
EFCC ta ce za a sake duba badaƙalar Matawalle na damfarar N70bn Hoto: EFCC, Bello Matawalle
Asali: Twitter

Mista Olukoyede ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu 2023 ta bakin daraktan hulda da jama’a na EFCC, Wilson Uwujaren.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ɗauki alkawarin sake buɗe kundin binciken karkatar N70bn ne biyo bayan zanga-zangar da wata ƙungiya 'Zamfara Alternative Forum' ta yi a hedkwatar EFCC da ke Jabi a Abuja.

Mambobin kungiyar sun mamaye hedikwatar EFCC ranar Juma’a don nuna rashin jin daɗinsu, kana suka buƙaci hukumar ta sake nazari kan binciken Matawalle.

Da yake jawabi yayin zanga-zangar, mai magana da yawun kungiyar, Mahmud Abubakar, ya bukaci hukumar EFCC da ta ci gaba da binciken tsohon gwamnan.

Zamu yi nazari kan badaƙalar Matawalle - EFCC

A rahoton Leadership, yayin da yake martani kan zanga-zangar, Uwujaren ya ce:

"Mun gode wa kungiyar Zamfara Alternative Forum da ta yi hakan cikin lumana. Muna son irin wannan zanga-zangar lumana da yunkurin matasan, ina tabbatar muku da cewa a EFCC babu wanda ya fi karfin doka.

Kara karanta wannan

Ganduje ya bayyana gwamnoni da 'yan majalisun tarayya da za su rungumi jam'iyyar APC

"Tun da shugaban hukumar EFCC ya kama aiki ya fara nazari da bankaɗo manyan kes ɗin da ya gada kuma ya ce na baku tabbacin cewa kes din da kuke ƙorafi ba zai zama shafaffe da mai ba.
"Za a sake duba lamarin, kuma shugaban EFCC na tabbatar muku da cewa za a yi wani abu bisa tanadin doka domin babu wanda ya fi karfin doka."

Matawalle ya yi rashin nasara a kotun ƙoli

A wani rahoton kuma kun ji cewa Bello Matawalle na APC ya sha kaye hannun Gwamna Lawal na PDP a hukuncin kotun koli.

Mai shari'a Agim, wanda ya jagoranci yanke hukuncin ya ce ɗan takarar APC, Bello Matawalle, ya gaza gamsar da kotu kan ikirarinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel