Dauda Vs Matawalle: Kotun Koli Ta Bayyana Sahihin Wanda Ya Ci Zaben Gwamna a Jihar Zamfara

Dauda Vs Matawalle: Kotun Koli Ta Bayyana Sahihin Wanda Ya Ci Zaben Gwamna a Jihar Zamfara

  • Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da Gwamna Dauda Lawal a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben jihar Zamfara a watan Maris
  • Kotun ta soke hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na ayyana zaben gwamnan a matsayin wanda bai kammala ba
  • Mai shari'a Agim, wanda ya jagoranci yanke hukuncin ya ce ɗan takarar APC, Bello Matawalle, ya gaza gamsar da kotu kan ikirarinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da Gwamna Dauda Lawal na jam'iyyar PDP a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Zamfara.

Kotun koli ta yi watsi da hukuncin kotun daukaka kara da ke Abuja wadda ta bayyana zaben gwamna Dauda Lawal a matsayin wanda bai kammala ba.

Kara karanta wannan

Bayan na Kano, Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar gwamnan PDP a Arewa, ta fadi dalili

Kotun koli ta yanke hukunci a shari'ar Zamfara.
Kotun Kolin Najeriya Ta Tabbatar da Nasarar Gwamna Dauda Lawal Na Zamfara Hoto: Dauda Lawal, Bello Matawalle
Asali: Facebook

Yayin yanke hukunci ranar Jumu'a, kwamitin alkalai biyar ya bayyana cewa daukaka karar da Gwamna Lawal ya yi ta dace, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukuncin da kotun koli ta yanke

Hukuncin da mai shari’a Emmanuel Agim ya yanke ya ce hukuncin kotun daukaka kara ya sabawa doka tare da sauya umarnin sake gudanar da zaben a wasu mazaɓun Zamfara.

Alkalin ya bayyana cewa ƙorafin Matawalle cewa sakamakon zaben kananan hukumomi uku, Birnin Magaji, Bukkuyum da Maradun da ya yi ikirarin ba daidai bane ya gaza gamsar da kotu.

Mai shari’a Agim ya yi bayanin cewa duk jam’iyyar da ta yi jayayya kan wani sakamakon zabe dole ne ta gabatar da sahihin sakamakon, Channels tv ta tattaro.

Yadda shari'ar ta faro daga kotun zaɓe

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Lawal a matsayin wanda ya lashe zaben, amma Matawalle ya kalubalanci nasarar da ya samu a kotu.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya maida martani bayan kotun ƙoli ta yanke hukunci, ya gode wa wanda ya ba shi nasara

Yayin da kotun sauraron kararrakin zabe ta tabbatar da nasarar gwamnan, kotun daukaka kara ta kore shi, kana ta umarci a sauya zaɓe a wasu akwatunan zaɓe.

Abban Kano ya gode wa Allah SWT

A wani rahoton kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya maida martani a karon farko bayan kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar da ya samu a zaben gwamnan Kano.

Ranar Jumu'a, 12 ga watan Janairu, kotun koli ta soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara kana ta tabbatar masa da kujerar gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel