Betta Edu: EFCC Ta Bugi Ruwan Cikin Manyan Jami’ai 10 Na Ma’aikatar Jin Kai, Bayanai Sun Fito

Betta Edu: EFCC Ta Bugi Ruwan Cikin Manyan Jami’ai 10 Na Ma’aikatar Jin Kai, Bayanai Sun Fito

  • Hukumar da ke yaki da masu yi wa dukiyar al'umma zagon kasa (EFCC) ta gayyaci wasu manyan jami'an ma'aikatar jin kai a jiya Laraba
  • An tattaro cewa, hukumar ta yi masu tambayoyi kan hannunsu a binciken da ta ke yi na yadda aka karkakatar da biliyoyin kudade daga ma'aikatar
  • Wata majiya daga hukumar ta ce jami'an sun bada hadin kai, inda suka amayar da wasu muhimman bayanai kan Edu da Umar-Farouq

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A jiya ne hukumar EFCC ta titsiye wasu manyan jami’ai goma na ma’aikatar jin kai da kawar da fatara yayin da ta kara fadada bincike kan zargin karkatar da kudaden gwamnati.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Kwanaki da dakatar da Minista, an gano Naira Biliyan 50 da ICPC ta bankado

Ana tuhumar Betta Edu bisa zargin bayar da umarnin biyan naira miliyan 585 da aka ware domin rabawa ‘yan Najeriya marasa galihu zuwa wani asusu na sirri.

EFCC ta dira kan manyan jami'an ma'aikatar jin kai
EFCC ta bigi ruwan cikin manyan jami’ai 10 na ma’aikatar jin kai, bayanai sun fito. Hoto: @Sadiya_farouq, @officialEFCC, @edu_betta
Asali: Twitter

Haka zalika ana tuhumar tsohuwar ministar ma'aikatar, Sadiya Umar-Farouq da kodinetar shirin NSIP, Halima Shehu kan karkatar naira biliyan 44, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda binciken EFCC ke gudana kan ma'akatar jin kai

A halin yanzu dai dukkan su matan uku na fuskantar tambayoyi a wajen hukumar da ke yaki da rashawar.

The Punch ta tattaro cewa jami’an hukumar EFCC sun karbo wasu karin takardu masu muhimmanci ga binciken daga wasu jami’an ma'aikatar.

A daren jiya, wani jami'in hukumar yaki da rashawar ya ce an gayyaci wasu manyan jami'an bankuna don su "tabbatar da rawar da suke takawa" a tafiyar da kudaden da jami'an ma'aikatar suka yi.

Kara karanta wannan

Badaƙala: EFCC ta tatsi muhimman bayanai, ta ɗauki mataki kan ministar da Tinubu ya dakatar

Jami'ai 10 da EFCC ta yi wa tambayoyi sun ba da muhimman bayanai

Baya ga manyan jami'ai guda 10, Dr. Edu da Halima Shehu sun sake fuskantar tambayoyi a jiya, yayin da ake sa ran hukumar za ta sake titsiye Hajiya Umar-Farouq a yau.

Majiyar ta ci gaba da cewa:

“Manyan jami’ai 10 sun yi bayani da yawa kan rawar da suka taka a cikin zargin da ake yi na hada-hadar kudaden.
“Wasu daga cikin jami’an sun yarda cewa sun ankarar da manyansu kan karkatar da kudaden amma aka yi watsi da korafinsu."

Kotu ta garkame tsohon ministan Obasanjo kan badakalar $6bn

A wani labarin makamancin wannan, wata babbar kotu da ke Abuja ta ba da umurnin garkame tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye a gidan gyaran hali na Kuje.

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Aguloye gaban kotun bisa zarginsa da karkatar da dala biliyan shida na aikin cibiyar wutar lantarki ta Mambila a zamanin mulkin Obasanjo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel