Ganduje Ya Bayyana Gwamnoni Da Ƴan Majalisun Tarayya Da Za Su Rungumi Jam'iyyar APC

Ganduje Ya Bayyana Gwamnoni Da Ƴan Majalisun Tarayya Da Za Su Rungumi Jam'iyyar APC

  • Dakta Abdullahi Ganduje ya bayyana shirinsa na ƙara yawan gwamnonin APC da yan majalisar tarayya
  • Shugaban APC na ƙasa ya ce jam'iyyar a karkashin jagorancinsa ba zata runtsa ba, zata ci gaba da aiki tukuru tsawon shekara
  • Ganduje ya kuma yi bayanin irin gyaran da APC take yi a cikin babbar sakariyarta ta ƙasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje, ya ce burinsa shi ne kara yawan gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki na jam'iyya mai mulki.

Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana haka ne yayin hira da ƴan jarida a birnin tarayya Abuja, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wasu ‘yan Arewa sun shiga kitsa yadda za a canza Ganduje a matsayin shugaban APC

Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Burinmu shi ne mu kara yawan gwamnonin APC, ‘yan majalisa – Ganduje Hoto: OfficialAPCNig
Asali: Twitter

A kalamansa, Dakta Ganduje ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tsarin mu shine mu kara yawan ‘yan majalisa da gwamnonin da muke da su na APC a kasar nan, kuma ta haka ne zamu samu ƙarin yawan ‘yan majalisar dokokin jihohi.
"Wannan ne ya sa muka kudiri aniyar cewa APC ba zata runtsa ba tsawon shekara saboda a al'ada an saba jam'iyyu na aiki ne kaɗai idan zabe ya zo.
"Amma a wuraren da demokuraɗiyya ta zauna da gindinta, jam'iyun siyasa suna aiki a kowane lokaci, ba zaɓe ne kaɗai fagensu ba har da ƙara yawan mambobi."

Ya ce jam’iyyar siyasa ta ƙunshi abu biyu domin ana sa ran za ta wayar da kan jama’a kan ci gaban da gwamnati ta samu tare da bayar da shawarwari kan manufofinta.

APC ta bullo sabbin abubuwa a sakateriyar Abuja

Ganduje ya ce ta haka ake tantance gwamnati, kana ya kara da cewa gyaran da ake yi da sabbin sabbin abubuwa da ake gani a sakatariyar APC ta kasa don ci gabanta ne da kasa baki daya.

Kara karanta wannan

"Burin kowane ɗan Najeriya ya ɗauki hoto da ni" Ministan Tinubu ya yi magana mai jan hankali

A rahoton PM News, Ganduje ya ci gaba da cewa:

"Kafin yanzu, babu coci a cikin sakatariyar mu, babu wanda ke iya zuwa coci a harabar, amma yanzu muna da sabon ginin coci da ake yi."
"Muna da shaguna ta yadda za mu guje wa cunkoso a kan titi a waje kuma muna da magudanar ruwa," in ji shi.

Kotun koli zata yanke hukuncu kan zaben Kuros Riba

A wani rahoton kuma Kotun koli ta gama sauraron ƙarar da jam'iyyar PDP ta kalubalanci nasarar Gwamna Bassey Otu na jihar Kuros Riba.

A zaman ranar Alhamis, kotun mai daraja ta ɗaya ta tanadi hukunci wanda ake sa ran za ta yanke ranar Jumu'a mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262