Yan Bindiga Sun Tashi Wani Kauyen Abuja Bayan Kashe Mutum 1 da Neman Fansar N5m

Yan Bindiga Sun Tashi Wani Kauyen Abuja Bayan Kashe Mutum 1 da Neman Fansar N5m

  • Sakamakon hare-haren 'yan bindiga, mutanen kauyen Yewuti da ke babban birnin tarayya Abuja sun yi hijira zuwa makwaftan garuruwa
  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun addabi garin da kai hari, inda ko a baya sai da suka kashe mutum daya da sace wasu da dama
  • A cikin wadanda aka sace ne aka biya Naira miliyan biyar kudin fansa, cikin mutanen har da mahaifin mataimakin shugaban karamar hukumar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Da yawan mazauna kauyen Yewuti da ke karamar hukumar Kwali, babban birnin tarayya Abuja sun yi hijira daga garin saboda hare-haren 'yan bindiga.

A baya-bayan nan ne dai 'yan bindiga suka kashe musu mutum daya tare da sako mutum hudu da suka sace bayan karbar Naira miliyan biyar da wasu kayayyaki abinci.

Kara karanta wannan

"Yan sanda sun yi garkuwa da ni, sun karbi Naira miliyan 1 kudin fansa", cewar Mr Soyemi

Yan bindiga sun tilasta mazauna kauyen Abuja yin hijira
Mazauna garin Yewuti da ke Abuja sun yi hijira zuwa Awawa, Abaji da kauyen Yongoji da Kwali sakamakon hare-haren 'yan bindiga.
Asali: Twitter

Hare-haren 'yan bindiga a kauyen Yewuti

Rahoton City & Crime na ranar 18 ga watan Nuwamba ya nuna cewa 'yan bindiga sun farmakin kauyen tare da sace mutum 8 ciki har da mahaifin mataimakin shugaban karamar hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai a ranar 2 ga watan Disamba suka sako mutu uku ciki har da mahaifin mataimakin karamar hukumar bayan karbar Naira miliyan biyar, Chronocle ta ruwaito.

Da ya ke tabbatar da kashe dan kauyen da kuma sako sauran mutum hudu, wani daga cikin iyalan wadanda abin ya shafa ya ce an sako 'yan uwansu a yammacin ranar Juma'a.

Abin da rundunar 'yan sanda ta ce kan wannan rahoto

Wani mazaunin garin, Shuaibu Aliyu, wanda ya zanta da wakilin Daily Trust a ranar Lahadi ya ce 'yan kauyen musamman mata da kananan yara sun yi hijira zuwa Awawa, Abaji da kauyen Yongoji da Kwali.

Kara karanta wannan

Ba a gama da jimamin kashe masu maulidi ba, 'yan bindiga sun yi kazamin barna a Bauchi

Ya ce:

"Wasu mazauna garin musamman manoma da suka yi hijira, na kwana a kauyen da ke kusa da mu, sai su dawo washe gari su yi aikin gona."

Da aka tuntube ta, kakakin rundunar 'yan sandan Abuja, SP Adeh Josephine, ta ce ba za ta iya yin magana kan lamarin ba sai dai kwamishina ne kawai zai iya cewa wani abu.

Mazauna garin Kaduna sun yi gudun hijira kan harin 'yan bindiga

A wani labarin makamancin wannan, gwamnati ta janye sojojin da ta girke a garin Magajin Gari ta uku da ke Birnin Gwari, jihar Kaduna.

Jim kadan bayan janye sojojin, 'yan bindiga suka farmaki mutanen garin inda suka rinka bi gida-gida suna karbar kudi da wayoyi kamar yadda wani mazaunin garin ya sanar.

Harin 'yan bindigar ya tilasta mazauna garin tserewa don kubutar da rayukansu, rahoton Legit Hausa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel