Yan Bindiga Sun Bada Wa'adin Kwana 7 Ga Iyalan Mutane 19 Da Suka Sace a Kaduna

Yan Bindiga Sun Bada Wa'adin Kwana 7 Ga Iyalan Mutane 19 Da Suka Sace a Kaduna

  • Yan bindiga su ba iyalan wadanda suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Kagarko, jihar Kaduna, wa'adin kwanaki bakwai su biya kudin fansa
  • Makwanni uku da suka gabata, ‘yan bindigan suka kai farmaki kauyen Kudiri, inda suka yi awon gaba da mutane 23, amma hudu sun kubuta a makon jiya
  • Yan bindigar sun nemi iyalan su tara masu kudin fansa naira miliyan 10 da buhunan shinkafa uku, ko kuma su zama silar asarar rayukan ‘yan uwansu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kagarko, jihar Kaduna - ‘Yan bindiga sun bayar da wa’adin kwanaki bakwai ga iyalan mutane 19 da suka yi garkuwa da su, akan su tara kudin fansa naira miliyan 10 da buhunan shinkafa uku, ko kuma su zama silar asarar rayukan ‘yan uwansu.

Kara karanta wannan

Yajin aikin NLC ya gamu da babban cikas a jihar Ƙaduna yayin da ma'aikata suka rabu gida biyu

City & Crime ta ruwaito cewa makwanni uku da suka gabata, ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Kudiri da ke karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da mutane 23.

Rundunar 'yan sanda
Masu garkuwa da mutanen, sun nemi a hada masu da kayan abinci, kuma suna bukatar hakan ne a cikin kwanaki bakwai Hoto: Nigerian Police
Asali: Facebook

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa, hudu daga cikin wadanda aka kama sun kubuta a makon jiya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu garkuwan, sun bukaci kudi da kayan abinci - Abdullahi

Wani dan uwan ​​daya daga cikin wadanda abin ya shafa, mai suna Abdullahi, wanda ya zanta da wakilinmu a ranar Litinin, ya ce shugaban ‘yan bindigar ya kira su ta wayar tarho a ranar Asabar.

Ya ce shuganan ya yi barazanar kashe mutanen 19 nan da kwana bakwai idan ba a biya musu bukatunsu ba.

Ya ce.

"Ko da yake shugaban 'yan bindigar ya nemi naira miliyan 20 tun da farko, amma bayan tattaunawa, ya rage kudin fansar a ranar Asabar da misalin karfe 11 na safe."

Kara karanta wannan

Babu Kudi: Takardun Nairori sun fara gagarar mutane a gari, duk da matakin CBN

"Wasu daga cikin dangin wadanda abin ya shafa sun fara sayar da kadarorin da suka mallaka, ciki har da amfanin gona, don tara kudaden."

Kawo yanzu dai babu wani martani daga kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna kan wannan rahoton.

Yan bindiga sun nemi kudin fansa daga iyalan wadanda suka sace a Abuja

A wani labari makamancin wannan, kun ji cewa, wadanda suka yi garkuwa da wasu mutane biyu mazauna unguwar Sabo a karamar hukumar Kuje, a babban birnin tarayya Abuja, sun bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 15.

Jaridar 'City and Crime' sun ba da rahoton cewa, makonni biyu da suka gabata, masu garkuwa da mutane sun farmaki yankin Sabo, tare da yin garkuwa da wasu mazauna garin, da aka bayyana sunayen su da Bissalla Yusuf da Mohammed Ibrahim.

Asali: Legit.ng

Online view pixel