Tarihi zai maimata kan sa: Sarki Sanusi II ya kama hanyar Sanusi I

Tarihi zai maimata kan sa: Sarki Sanusi II ya kama hanyar Sanusi I

Muhammadu Sanusi 1 shi ne Kakan Sarkin yanzu Sarki Muhammadu Sanusi II wanda yake samun sa-in-sa da gwamnati a halin yanzu. A 1963 ne gwamnan Arewa Kashim Ibrahim ya sanarwa Sarki Sanusi I cewa zai bar gadon sarauta.

Tarihi zai maimata kan sa: Sarki Sanusi II ya kama hanyar Sanusi I

Sarki Sanusi II ya kama hanyar Kakanninsa a kan sarautar Kano
Source: Twitter

Gwamnatin Sardauna ta dauki matakin tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I daga kan gadon mulki ne bayan sun samu sabani. Kashim Ibrahim ne ya kawowa Sarkin takardar murabus daga ofishin Sardauna domin ya sa hannu.

Nan-take Sarki Sanusi I ya rattaba hannu ba tare da ya ji wani dar-dar ba inda bayan ya sa-hannu aka nemi ya bar Kano zuwa wata kasa. A nan ne Mai martaban ya zabi ya wuce kasar Azare, inda ya karasa rayuwar sa har ya bar Duniya.

KU KARANTA: Sunayen sababbin Sarakunan da za a nada a Kasar Kano

A wata takarda da wani Masanin tarihi Ajiroba Yemi Kotun ya rubuta mai suna “Road to Azare: How Emir Sanusi’s Grandfather Was Removed Due To ‘Jealousy." yace kishi ne ya jawo aka sauke Sarkin Kano na lokacin daga kan mulki.

A lokacin Ahmadu Bello yana Firimiyan Arewa, shi kuma Sarki Sanusi I shi ne Mukaddamin Darikar Tijaniyyah a Najeriya, a dalilin kusancin sa da Shehi Ibrahim Inyaas, shi kuma a lokacin Sardauna yana jan ragamar Darikar Qadriyyah.

Sardauna a wancan lokaci shi ne babban Jagoran Qadriyyah a Arewacin Najeriya, wanda wannan ya jawo banbancin ra’ayi tsakaninsa da Sanusi I. Ahmadu Bello a lokacin yana kokarin kafa kan sa a matsayin Jagoran addini a Arewa.

KU KARANTA: Ganduje ya sheka Abuja bayan hakar sa ta gaza cin ma ruwa

Yunkurin da Firimiya Ahmadu Bello yake yi na mamaye Musulman Arewa ne ya jawo sabani da Sarkin na Kano wanda a lokacin yake samun goyon baya da girma daga dubban Mabiya Tijjaniya wanda ya zama kalubale ga Firimiyan Yankin.

Muhammadu Sanusi I shi ne babban ‘Dan da Abdullahi Bayero ya bari a lokacin da ya rasu. Bayan tsige sa ne aka nada Sarki Inuwa wanda ya rasu ba da dadewa ba, sai aka nada Ado Bayero a karshen 1963.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel