Fasto Ya Yafewa Masu Zuwa Cocinsa Biyan Kudin Baiko Saboda Kuncin da Ake Ciki a Najeriya

Fasto Ya Yafewa Masu Zuwa Cocinsa Biyan Kudin Baiko Saboda Kuncin da Ake Ciki a Najeriya

  • Wani babban malamin coci ya bayyana cewa, ba zai kuma karbar kudin baiko ba a hannun masu zuwa cocinsa
  • Ya ce yanayin da ake ciki a Najeriya ne ya sanya yin wannan shawari, kuma ya yi kira kowa ya yi koyi da shi
  • Wannan lamari ya dauki hankalin jama'a a kafar sada zumunta, inda jama'a da dama ke yaba wa wannan malamin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Legas - Bidiyon wani fastocin cocin da ya sanar da dakatar da karbar kudin baiko a cocinsa ya yadu a kafar sada zumunta kwanan nan.

Faston wanda ya aika sakon ga jama’arsa ta harshen Turanci da Yarbanci ya ce halin da ake ciki kuncin rayuwa a kasar nan ne ya sa ya janye karbar baikon.

Kara karanta wannan

Jonathan ya bayyana abu 1 da zai hana 'yan siyasa zuwa kotu idan sun fadi zabe

Fasto ya daina karbar baiko a cocinsa
Yadda fasto ya daina karbar baiko a cocinsa | Hoto: @hmusaabk (X), GettyImages
Asali: UGC

Ya kara da cewa, dakatar da baikon ba yana nufin fastoci za su kwana da yunwa bane, ya kara da cewa za su tsira daga abin da Allah ya mallaka masu, The Guardian ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Na daina karbar baiko a coci na, inji fasto

Limamin wanda ya yi jawabi ga ’yan cocinsa da ke murna da jin matakinsa, ya kuma yi mika ga sauran limaman coci a kasar nan su yi irin abin da ya yi, Daily Trust ta ruwaito.

Da yake jawabi, ya ce:

"Kada ku karbi kudin baiko a yau, ya zuwa yanzu saboda yanayin da ake ciki a kasar nan. Yanzu dai mun janye karbar baiko."

Fastoci su daina karbar kudin baiko

Ya kuma ja hankalin sauran masu sana'a irin tasa da cewa:

"Ya kamata fastoci su gane su dakatar da karbar baiko duba da yanayin kasar nan, ya kamata mu daina karbar baiko.

Kara karanta wannan

Kaduna: An shiga tashin hankali, wata amarya ta datse mazakutar angonta

"Dalili kuwa, mutum zai iya kashe N1000 kudin sufurin zuwa coci, kuma a haka ya ba da baiko sannan ya koma da kafa.
"Kun fahimce ni? Rashin ba da baiko bai nufin fasto zai kwana da yunwa, idan dai Allah ya kira shi. Amma yanzu kam, har zuwa lokacin da farashin mai zai sauka... babu batun karbar baiko a cocin nan."

Wani ya yi barazanar kai coci kotu kan kudin baiko

A bangare guda, wani mutum ya rubutawa wata coci bukatar a dawo masa da duk abin da ya bayar a matsayin baiko da sadaka ga cocin tsawon shekara 19.

Dishon Kinyanjui Kinuthia, wani kirista dan Kenya, ya rubata wasikar ta shafin Tuwita ga Cocin kuma ya yi gargadin cewa zai dauki mataki idan ba'a dawo masa da kudadensa ba.

Dishon, wanda ya ke halartar Cocin Revival Mission Church, Kabete, a Nairobi, ya ce ya kasance yana halartar cocin daga shekarar 1997 kafin ya bar cocin a 2018.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.