Innalillahi: Babbar Mota Ta Murkushe Motoci 4, Mutane da Yawa Sun Mutu a Jihar Imo

Innalillahi: Babbar Mota Ta Murkushe Motoci 4, Mutane da Yawa Sun Mutu a Jihar Imo

  • Wata babbar mota ta yi sanadiyyar mutanr da dama a jihar Imo biyo bayan yadda ta murkushe wasu motocin bas guda hudu
  • Shaidun gani da ido sun tabbatar da yadda lamarin ya faru da kuma irin tashin hankalin da dangi suka shiga bayan hadarin
  • Ana yawan hadurran mota a jihohin Najeriya musamman duba da yadda hanyoyi ke lalacewa da kuma rashin gyara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Imo - Akalla mutane 15 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata bayan da wata babbar mota ta afkawa kananan motocin bas guda hudu a birnin Owerri, babban birnin jihar Imo.

Kara karanta wannan

CNG: Manyan matakai 3 da Tinubu ya dauka na janye Najeriya daga dogara da man fetur

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:30 na dare a ranar Asabar a magamar Jami’ar Jihar Imo, IMSU.

Hadari ya ci mutum 15 a jihar Imo
Yadda hadari ya kashe mutum 15 a jihar Imo | Hoto: Premium Times, GettyImages (Klaus Vedfelt)
Asali: UGC

Shaidun gani da ido sun shaidawa jaridar Premium Times, cewa da alama motar ta samu matsala a birki ne wanda ya kai ga aukuwar hadarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayani daga shaidun gani da ido

Chinedu Opara, wani ganau, ya ce:

"Muna tunanin motar ta samu matsalar birki ne, daga nan ta fada kan wasu kananan motocin bas da ke lodi a magamar.”

Wani ganau kuma mai suna Chika Nwosu, ya ce babbar motar ta yi aron hannu ne wanda daga karshe ta fada kan motocin bas din.

Wani dan jarida mai suna Chidiebube Okeoma a jihar ya yada wasu faifan bidiyo na lokacin da lamarin ya auku.

An shiga jimamin rashin ‘yan uwa

A wasu faifan bidiyo da Premium Times tace ta gani, wasu mutane sun yi ta kukan rashin ‘yan uwansu a hadarin.

Kara karanta wannan

An kame satasan da suka yi amfani da bindigar sasan yara wajen Sace mota a Enugu

Ya ce ya taimaka wajen kai wadanda abin ya shafa asibitoci daban-daban, amma wasu daga cikinsu sun mutu.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Henry Okoye da safiyar ranar Lahadi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Yadda hadari ya kashe jama'a a Ogun

A wani labarin, mutane shida ne ciki har da mata da kananan yara suka rigamu gidan gaskiya a wasu jerin haduran mota a jihar Ogun.

Mutane akalla 21 ne suka jikkata yayin da motocin suka yi karo da juna a kan hanya.

Jami'ar hulda da jama'a ta hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen jihar Ogun, Florence Okpe, ce ta bayyana wuraren da haduran suka faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.