'Yan Sanda Sun Kama Chinasa Nwaneri, Tsohon Mai Taimaka Wa Gwamna Uzodinma

'Yan Sanda Sun Kama Chinasa Nwaneri, Tsohon Mai Taimaka Wa Gwamna Uzodinma

  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan sanda sun kama Nze Chinasa Nwaneri a wani otel da ke Owerri, babban birnin jihar Imo
  • Nze Chinasa Nwaneri ya kasance tsohon mai baiwa Gwamna Hope Uzodimma shawara kan ayyuka na musamman
  • Har yanzu ba a gano dalilin da yasa aka kama Nwaneri ba, amma an ce yana daya ɗaya daga cikin amintattun Uzodimma a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Imo - 'Yan sanda masu binciken kwakwaf sun kama tsohon mai baiwa Gwamna Hope Uzodimma shawara kan ayyuka na musamman, Nze Chinasa Nwaneri a Imo, babban birnin jihar.

An kama tsohon hadimin Gwamna Uzodimma
'Yan sanda sun kama tsohon na hannun daman gwamnan jihar Imo. Hoto: @Hope_Uzodimma1
Asali: Twitter

Nwaneri ya kasance ɗaya daga cikin amintattun mataimakan Uzodimma waɗanda suka kasance tare da shi sama da shekaru goma sha biyar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake ba babban mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale sabon mukami

An kama Nze Nwaneri a otel

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an kama Nwaneri ne a otal din RockView da ke Owerri ranar Asabar kuma an kai shi hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wata majiyar, an mayar da Nwaneri zuwa dakinsa na otal din inda aka yi bincike sosai kafin a mayar da shi ofishin ‘yan sandan.

Har zuwa lokacin da aka wallafa wannan labarin, ba a gano ainahin dalilin da yasa aka kama shi ba.

Karashen labarin na tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.