Yan Bindiga Sun Kai Hari a Hedikwatar Babbar Karamar Hukuma a Zamfara

Yan Bindiga Sun Kai Hari a Hedikwatar Babbar Karamar Hukuma a Zamfara

  • Garin Kauran-Namoda hedikwatar ƙaramar hukumar Kauran-Namoda ya fuskanci harin miyagun ƴan bindiga
  • Miyagun ƴan bindigan sun farmaki garin ne da misalin ƙarfe 9:00 na dare inda suka salwantar da rayukan mutum biyu
  • Dakarun sojojin atisayen 'Operation Hadarin Daji' da ke a garin sun samu nasarar fatattakar ƴan bindigan bayan sun gwabza artabu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Rayukan mutum biƴu sun salwanta a wani harin da ƴan bindiga ɗauke da makamai suka kai a jihar Zamfara.

Miyagun ƴan bindigan sun kai harin ne a garin Kauran-Namoda, hedikwatar ƙaramar hukumar Kauran-Namoda ta jihar Zamfara.

Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
Yan Bindigan sun halaka mutum 2 a yayin harin Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Yadda harin ya auku

A cewar wani ganau ba jiyau ba, ƴan bindigan sun mamaye garin ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Talata, 21 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun dauki mataki mai tsauri kan masu ba yan bindiga bayanai a jihar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa ƴan bindigan na shigowa suka fara harbe-harbe lamarin da ya tilastawa mazauna garin tserewa domin tsira da rayukansu.

Wani mazaunin garin Kauran-Namoda mai suna Ismaila Kaura ya shaida wa Channels tv cewa an kashe mutum biyu a harin da ƴan bindigan suka kawo.

Ya ce daga cikin mutum biyun da suka rasa rayukansu har da wata ɗaliba mai suna Ni'ima wacce ke kan hanyarta ta zuwa makarantar Islamiyya a lokacin.

Ya ce dakarun sojojin atisayen 'Operation Hadarin Daji' da aka tura garin sun yi artabu da ƴan bindigar tare da tilasta musu barin garin.

Har yanzu dai rundunar ƴan sandan jihar ba ta ce uffan ba dangane da sabon harin.

Ƴan bindiga sun sace matar dagaci

Miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen Ruwandorawa cikin ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara, inda suka sace matar dagacin ƙauyen tare da wasu mutum 15.

Kara karanta wannan

Nasara: Dakarun sojoji sun buɗe wa tawagar 'yan bindiga wuta, sun kashe su da yawa a arewa

Ƴan bindigan a yayin harin sun kuma halaka wani jami'in ɗan sanda mai aiki a ofishin ƴan sanda na ƙauyen.

Ƴan Bindiga Sun Sace Matan Aure

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki a ƙauyen Gwombe cikin ƙaramar hukumar Kuje ta birnin tarayya Abuja.

Ƴan bindigan a yayin harin sun sungume wasu matan aure takwas lokacin da su ke tsaka da gudanar da aiki a gona.

Asali: Legit.ng

Online view pixel