Dakarun Sojoji Sun Dauki Mataki Mai Tsauri Kan Masu Ba Yan Bindiga Bayanai a Jihar Arewa

Dakarun Sojoji Sun Dauki Mataki Mai Tsauri Kan Masu Ba Yan Bindiga Bayanai a Jihar Arewa

  • Dubun masu ba ƴan bindiga bayanai a jihar Kaduna ta cika bayan dakarun sojoji sun yi caraf da su a garin Kagarko
  • Masu ba ƴan bindigan bayanai da aka cafke an same su da tabar wiwi, ƙwayoyi da maƙudan kuɗaɗe a tattare da su
  • Miyagun mutanen bayan sun sha dukan tsiya sun amsa cewa ƴan bindiga ne suka aike su domin siyo musu kayayyakin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Dakarun sojoji sun kama wasu mutum uku da ake zargin masu ba ƴan bindiga bayanai ne a wani shingen bincike mai nisa kaɗan da garin Kagarko, hedikwatar ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.

Wani mazaunin Kagarko, Mu’azu Abdullahi, a ranar Laraba, 22 ga watan Nuwamba ya bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 6:00 na yamma, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

"Bai yiwuwa kana da N1m ka ba ubangiji sadakar N500": Hudubar fasto ta jawo cece-kuce

Sojoji sun cafke masu ba yan bindiga bayanai
Dakarun sojoji sun yi caraf da masu ba yan bindiga bayanai a Kaduna Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Su ukun suna saman babur ne sai sojojin da ke shingen binciken suka yi shakku, a yayin da ake duba su, an gano wata jaka ɗauke da tabar wiwi da kuɗi da ba a bayyana adadinsu ba a jikin ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin."

Ya ce daga baya waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu yayin da ake yi musu dukan tsiya da cewa wasu ƴan bindiga ne suka aike su domin su siyo musu tabar wiwi, ƙwayoyi da giya, rahoton Trust Radio ya tabbatar.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wata mazauniyar jihar Kaduna, mai suna Malama Saida, wacce ta yaba da wannan namijin ƙoƙarin da sojojin suka yi.

Ta bayyana wannan abun a yaba ne domin masu ba ƴan bindiga bayanai hatsabiban mutane ne waɗanda suke ƙara taɓarɓarar da lamuran tsaro.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun halaka direba tare da yin awon gaba da fasinjoji a wani sabon hari

"Waɗannan miyagun dama bai kamata ana barinsu da rai ba domin suna da matuƙar hatsari a cikin al'umma, saboda suna zaune tare da mutane a cikin gari." A cewarta.

Ƴan bindiga sun nemi a kawo kuɗin fansa

A halin da ake ciki kuma ƴan bindigan da suka sace mutum 19 da suka haɗa da ƴaƴan Fasto uku a ƙauyen Kudiri da ke yankin sun bukaci iyalai da ƴan uwan ​​mutanen da su tara Naira 800,000 domin kowannensu kafin a sako su.

Wani ɗan uwan ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, Kabiru Alhassan, a ranar Laraba, ya ce buƙatar na zuwa ne duk da cewa mutanen ƙauyen sun haɗa Naira 550,000 domin siyan kayan abinci da magunguna da kuma giya ga ƴan bindigan.

Kawo yanzu dai babu wani martani daga kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna kan kamen da sojoji suka yi wa mutum ukun.

Ƴan Bindiga Sun Sungume Hakimi

Kara karanta wannan

Ana jimamin harin sajoji kan masu mauludi, dakarun sojoji sun sheke masu ba yan bindiga bayanai

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari a garin Kujama cikin ƙaramar hukumar Chikun a jihar Ƙaduna inda suka sace Hakimin garin.

Ƴan bindigan sun sace Steven Ibrahim ne tare da wasu mutane biyu yayin da su ke fitowa daga wani wajen shaktawa da ke bayan makarantar Bethel Baptist.

Asali: Legit.ng

Online view pixel