'Yan Bindiga Sun Bindige Dan Sanda, Sun Sace Matar Dagaci da Wasu Mutane 15 Yayin Wani Farmaki

'Yan Bindiga Sun Bindige Dan Sanda, Sun Sace Matar Dagaci da Wasu Mutane 15 Yayin Wani Farmaki

  • Mahara sun kai hari kauyen Ruwandorawa a karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara inda su ka sace mutane da dama
  • Lamarin ya faru ne a tsakar daren ranar Lahadi 19 ga watan Nuwamba inda su ka sace matar dagacin kauyen
  • Wata majiya ta tabbatar da cewa maharan sun samu shiga gidan dagacin ne bayan harbe wani dan sanda da ke gadin gidan har lahira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Zamfara - 'Yan bindiga sun yi ajalin wani jami'in dan sanda tare da sace matar dagaci a jihar Zamfara.

Maharan sun yi ajalin dan sandan da ke ofishin 'yan sanda a yankin Ruwandorawa da ke karamar hukumar Maru a jihar.

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a gidan Shehu Shagari tsohon shugaban kasar Najeriya

'Yan bindiga sun yi ajalin dan sanda tare da sace matar dagaji a jihar Zamfara
Maharan sun sace matar dagaci bayan hallaka dan sanda. Hoto: Dauda Lawal Dare.
Asali: Facebook

Yaushe 'yan bindigan su ka kai hari?

Har ila yau, maharan sun sace wasu mutane 15 tare da matar dagacin kauyen yayin harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Channels TV ta tattaro cewa maharan sun kai harin ne da tsakar daren ranar Lahadi 19 ga watan Nuwamba.

Wata majiya ta tabbatar da cewa 'yan bindigan sun yi ta harbe-harbe kafin su bindige dan sandan da ke kokarin kare gidan dagacin garin.

Majiyar ta ce maharan sun zo da niyyar sace dagacin garin ne amma ba su iske shi ba sai su ka sace matarsa.

Mene martanin 'yan sanda kan harin?

A cewar majiyar:

"Sun samu damar shiga gidan dagacin bayan harbe dan sandan da ke gadin gidan.
"Ba su samu damar dauke dagacin ba yayin da su ka yi awun gaba da matarsa."

Rahotanni sun tabbatar cewa har yanzu maharan ba su tuntubi wadanda abin ya shafa ba don biyan kudin fansa, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan 'Boko Haram' sun budewa ayarin motoccin Gwamna Buni wuta, rayuka sun salwanta

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Yazid Abubakar ya ci tura saboda rashin samun wayarsa a lokacin tattara wannan rahoto.

Sojoji sun kai samame maboyar Boko Haram a Kaduna

A wani labarin, rundunar sojin sama ta yi ruwan wuta kan maboyar kwamandan Boko Haram inda su ka hallaka mayaka da dama.

Rundunar ta kai harin ne a karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna bayan samun bayanan sirri da al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel